Biyo bayan mummunan rushewar ginin makarantar Saint Academy a Busa Buji, Jos, Jihar Filato, a ranar Juma’a, 12 ga Yuli, 2024, Gwamnatin Tarayya ta ƙaddamar da bincike na gaggawa. Ministan Gidaje da Ci gaban Birane, Arc. Ahmed Musa Dangiwa, ya umarci Shugaban Gudanarwar Gidaje na Tarayya a Jihar Filato da ya gudanar da bincike mai zurfi don gano musabbabin rushewar ginin da tabbatar da cewa wadanda suke da hannu za su fuskanci hukunci.
Minista Dangiwa ya nuna matuƙar damuwarsa game da wannan lamari, yana mai jaddada cewa matsalar rushewar gine-gine a Nijeriya na faruwa ne sakamakon sakacin da ake yi yayin gini. Ya jaddada irin tasirin da irin wannan ibtila’in ke da shi ga iyalai da al’ummomi, kasancewar hakan kan haifar da asarar rayukan mutane marasa laifi. Dangiwa ya tabbatarwa da jama’a cewa wannan bincike zai kasance mai zurfi, kuma duk wanda aka samu da laifi zai fuskanci hukunci na doka, domin hana aukuwar irin wannan abu a nan gaba.
- Wani Matashi Ya Yi Barazanar Faɗowa Daga Dogon Ƙarfen Gidan Rediyo A Abuja
- Kotu Ta Tura Tsohon Ministan Wutar Lantarki Zuwa Gidan Yari
Haka zalika, Dangiwa ya yi nuni da ƙudirin ma’aikatar wajen hana aukuwar rushewar gine-gine a nan gaba ta hanyar tabbatar da bin ƙa’idoji da dokokin gini. Ya bayyana haɗin gwuiwar da ake yi da hukumomin da suka dace da kuma aiwatar da hanyoyin kula da bin dokokin gini, musamman ga ayyukan Renewed Hope Cities and Estates, a matsayin shaida kan jajircewar ma’aikatar wajen tabbatar da ingantattun tsare-tsaren gini a faɗin ƙasar.