Gwamnatin Tarayya ta ɓullo da sauye-sauye a fannin ilmin fasaha da nufin samarwa matasan Nijeriya da sana’o’in hannu da kuma daidaita tsarin ilimi na kasar da ka’idojin makarantantun ilimi na duniya.
An bayyana hakan ne a wata sanarwa mai ɗauke da kwanan watan Satumba 10, 2025, da sa hannun Daraktan yada labarai da hulda da jama’a na ma’aikatar ilimi ta tarayya, Boriowo Folasade.
- ‘Yansanda Sun Cafke ‘Yan Fashi 3 A Kano, Sun Ƙwato Motar Sata
- Tinubu Ya Bayar Da Umarni Karya Farashin Kayan Abinci A Nijeriya
Ɗaya daga cikin hadiman shugaban kasa Bola Tinubu kan harkokin yada labarai, Dada Oluwasegun, wanda ya sake yada labaran a shafinsa na Facebook a ranar Alhamis, ya ce sake fasalin na daga cikin babban sauyi ne na bankwana da tsohon tsarin da “takarda kawai ake bukata”.
Ministan Ilimi, Dr. Maruf Tunji Alausa, tare da Karamar Ministar Ilimi, Farfesa Suwaiba Sa’id Ahmad, ne suka sanar da sabon tsarin a ranar Laraba, inda suka bayyana shi a matsayin wani ƙwaƙƙwaran mataki na “rage yawan masu neman aiki a ma’aikatun gwamnati da na masu zaman kansu, ta hanyar koyar da dabarun kasuwanci, daidai da ka’idojin duniya, da kuma shirya matasan Nijeriya don samun ayyukan yi a nan gaba.

Kwasakwasai na koyar da dabarun Kasuwanci 26 da gwamnatin ta bullo da su, sun hada da Brick Laying, Block Laying and Concreting, Painting Decoration and Finishes (Interior Design), Woodwork, Carpentry and Joinery, Welding & Fabrication, Plumbing and Pipe Fitting, Computer Hardware & GSM Repair and Maintenance, Auto-Mobile Mechanics, Refrigeration & Air-conditioning Works, Mechanized Agriculture (Mechanics/Operations/Smart Agriculture), Autobody Works, Catering Craft Practice, Solar PV Installation and Maintenance and Fashion Design and Garment Making
Sauran su ne, Livestock Farming/Animal Husbandry, Fish Farming Activity (Aquaculture), Motorcycle & Tricycle Repairs, Auto-Electrical Wiring, Beauty Therapy & Cosmetology, Creative Media (Digital Media Production), Electronic Systems Maintenance Craft, Furniture Making & Upholstery, Networking & System Security (Satellite TV Antenna installation and maintenance), Social Media Content Creation and Management, Tiling & Cladding (Decorative stonework/Floor cover installation), Automobile CNG Conversion and Maintenance and Leather Works.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp