Gwamnatin tarayya ta amince da ba da kwangilar gina wasu manyan hanyoyi da za su lakume naira Tiriliyan 4.2, da za su kunshi shimfida manyan tituna da gadoji a sassan kasar nan.
Ministan ayyuka, David Umahi, shi ne ya sanar da hakan a karshen zamanin majalisar zartarwa wadda Shugaban kasa Bola Tinubu ya jagoranta a ranar Litinin a Abuja.
- Gidaje Da Dabbobi Sun Ƙone A Yayin Da Gobara Ta Tashi A Wani Ƙauyen Kano
- Tunawa Da Ranar Wadanda Aka Yi Wa Kisan Kiyashi: Majalisar Dinkin Duniya Ta Wayar Da Kan Dalibai A Abuja
A cewar Umahi, wadannan ayyukan sun shafi jihohi da dama, da aka yi da manufar inganta hada can da nan, inganta tsaron rayuka a kan hanyoyi, da kuma kyautata ci gaban tattalin arziki.
Kwangilolin sun hada da gina wasu sabbin tituna, kwaskwarima ga wasu da suka lalace da fadada wasu hanyoyin.
Kaso mafi tsoka ya tafi ne kan aikin shimfida katafare kuma babban hanya daga Legas zuwa Kalabar, inda majalisar zantarwar ta amince da kashe naira tiriliyan 1.334 domin gina babban tagwayen titi mai nisa kilomita 130.Â
Wannan ya hada da kilomita 65 daga Legas zuwa Ogun da wani karin da zai tashi daga Kalabar ta Akwa Ibom, wanda titin zai ginu a karkashin ‘Engineering, Procurement, and Construction’ (EPC) da tsarin za su kula da shi na tsawon shekaru goma bayan ginawa.
Majalisar zartarwar ta amince da kashe naira biliyan 470.9 domin gina hanyar da ta nausa Jihar Delta da kuma wani naira biliyan 148 don gina hanya a Jihar Anambra zuwa gada ta biyu a Neja.
Shi kuma babban hanyar Lagos zuwa Ibadan ya samu amincewar naira biliyan 195 domin a gina shi a karkashin asusun shirin inganta hanyoyi na shugaban kasa (PIDF), da ke da manufar rage cunkoso da inganta sufuri a manyan hanyoyin da ake yawan bi.
Sai dai hanyar Abuja zuwa Kano wanda aka jima da bayar da shi ga kamfanin ‘Julius Berger’, yanzu an sake fasalta shi yadda za a samu nasarar kammala aikin a kan lokaci. Ministan ya ce yanzu aikin ya koma kilomita 118 kuma za a sanya wutar layi.
Ministan ya ce dukkanin ayyukan masu inganci ne za a yi kuma da nufin kyautata rayuwar al’ummar kasa da kare rayukan a yayin tafiye-tafiye, ya ba da tabbacin gwamnati na sanya ido wajen gudanar da nagartaccen aiki.