Gwamnatin Tarayya ta ayyana ranar Laraba, 1 ga watan Oktoba, 2025, a matsayin hutu don bikin cikar Nijeriya shekara 65 da samun ’yancin kai.
Ministan Harkokin Cikin Gida, Olubunmi Tunji-Ojo, ya taya ’yan Nijeriya murna tare da buƙatar su ci gaba da nuna kishin ƙasa, haɗin kai da juriya.
- Kasashen Sin Da Afrika Za Su Hada Kai A Bangaren Intanet
- Kotu Ta Dakatar Da PENGASSAN, NNPCL Kan Katse Wa Matatar Ɗangote Ɗanyen Mai Da Iskar Gas
Haka kuma ya buƙaci ’yan kasa da su mara wa Shugaba Bola Tinubu baya, inda ya mayar da hankali kan farfaɗo da ƙasa, bunƙasa tattalin arziƙi, da ci gaba.
Ministan ya bayyana tabbacin cewa idan aka haɗa kai, Nijeriya za ta ci gaba da samun zaman lafiya, da ci gaban tattalin arziƙi.
Ya yi wa ’yan Nijeriya fatan gudanar da biki mai cike da annashuwa, tare da kira da a yi tunani kan tafiyar da aka yi tun daga samun ’yanci, sannan a haɗa hannu wajen gina makoma mai kyau.