Gwamnatin tarayya ta sanar da dakatar da bude sabbin jami’o’in gwamnatin tarayya, da kwalejojin fasaha, da kwalejojin ilimi na kasar nan na tsawon shekaru bakwai.
Matakin ya kasance wani yunkuri mai mahimmanci don magance tabarbarewar inganci da ababen more rayuwa a fannin ilimin manyan makarantu na kasar.
- Aikin Hakar Kwal Ta Hanyar Amfani Da Fasahar Zamani Ya Fara Wuce 50% a Kasar Sin
- Tinubu Ya Taya Nafisa, Rukayya, Hadiza Murnar Samun Nasarar Zama Gwanaye A Gasar Turanci Ta Duniya
Ministan Ilimi, Dokta Tunji Alausa ne ya bayyana haka ga manema labarai a fadar gwamnati bayan taron majalisar zartarwa ta tarayya da aka yi a ranar Laraba wacce shugaba Bola Tinubu ya jagoranta a fadar shugaban kasa da ke Abuja.
Alausa ya ce dakatarwar, wacce ta shafi dukkan nau’o’in manyan makarantun gwamnatin tarayya an yi hakan ne da nufin dakatar da maimaici da barnatar da dukiyar gwamnati, inda za a yi amfani da kudin domin inganta makarantun da ake da su.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp