Gwamnatin tarayya ta fara shirin kwaso ‘yan Nijeriya da ke zaune a kasar Lebanon, biyo bayan barkewar rikici tsakanin Isra’ila da Iran.
Mai bai wa shugaban kasa shawara kan al’amuran kafafen sadarwa na zamani, Dada Olusegun ne, ya bayyana haka a ranar Talata.
Ya bukaci ‘yan Nijeriya da ke zaune a Lebanon da su tuntubi ofishin Jakadancin kasar don su ba da bayanansu.
- Mutane 25 Sun Rasu A Hatsarin Jirgin Ruwan Neja – NSEMA
- Sin Ta Bukaci NATO Da Ta Gyara Mummunan Tunaninta Game Da Kasar Sin
A wani sakon da ya kafa a shafinsa na X, ya ce gwamnatin Nijeriya ba ta bayanan mutanen da ke zaune a Lebanon.
A ranar Talata, Iran ta harba makamai masu linzami 180 cikin Isra’ila a matsayin martani kan kisan shugabanin Hezbollah.
Kasashen biyu sun yi ta barazana a tsakaninsu bayan ruwan makamai masu linzamin da Tehran ta yi.
Firaministan Isra’ila, Beyamin Netanyahu, ya lashi takobin mayar da martini mai zafi a kan harin da aka kai Isra’ila.
A nasu bangaren kuma, kasar China da Saudiyya sun yi kira da a kwantar da wannan tarzomar da ta ke dada ruruwa a yankin Gabas ta Tsakiya.
Sannan, sun yi kira ga bangarorin biyu da su dawo kan teburin sulhu.