Gwamnatin tarayya ta gargadi ƙungiyar malaman jami’o’i ta ƙasa (ASUU) da ta guji shiga yajin aiki, tana mai jaddada cewa dokar “babu aiki, babu albashi” tana nan daram. Ministan Ilimi, Dr. Maruf Tunji Alausa, tare da ƙaramin Ministan Ilimi, Farfesa Suwaiba Sai’d Ahmed, sun bayyana haka a cikin wata sanarwa da Daraktan Yaɗa Labarai na Ma’aikatar Ilimi ta Tarayya, Boriowo Folasade, ya fitar a ranar Lahadi.
Ministocin sun tabbatar da cewa gwamnati na ci gaba da tattaunawa mai ma’ana da ASUU domin warware duk wasu matsaloli da ke addabar tsarin jami’o’i a Nijeriya. Sun bayyana cewa gwamnati ta nuna gaskiya da haƙuri a tattaunawarta da ƙungiyar, inda ta riga ta amince da mafi yawan buƙatun ASUU, ciki har da ƙarin wani kaso na alawus ɗin koyarwa da inganta yanayin aiki na malamai.
- Yanzu-Yanzu: ASUU Ta Tsunduma Yajin Aiki Na Tsawon Mako Biyu
- ASUU Ta Bai Wa Gwamnatin Tarayya Wa’adin Kwanaki 14 Don Biyan Buƙatunta
Sun kuma jaddada cewa dokar “babu aiki, babu albashi” tana nan tana aiki bisa tsarin doka, kuma gwamnati ba za ta lamunci gaza bin doka ba idan aka sake katse ayyukan ilimi a jami’o’i. Sun ƙara da cewa sauran ‘yan matsalolin da suka rage suna ƙarƙashin ikon kwamitocin gudanarwa na jami’o’i, waɗanda aka sake kafa su don magance irin waɗannan batutuwa.
Ministocin sun bayyana damuwa cewa duk da cikar wa’adin da gwamnati ta bayar wajen gabatar da matsayinta, ASUU ta ci gaba da shirin yajin aiki maimakon komawa tattaunawa. Sun ce wannan mataki ba ya nuna haɗin kai ko adalci ga ɗalibai da al’umma, musamman ganin irin matakan da gwamnati ta ɗauka.
Sun tabbatar da cewa ƙarƙashin shirin Renewed Hope na Shugaba Bola Ahmed Tinubu, gwamnati na da niyyar tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a tsarin ilimi, tare da kira ga ASUU da ta koma teburin tattaunawa domin kauce wa sake gurgunta kalandar karatu a jami’o’in ƙasar.