Ma’aikatar Harkokin Wajen Nijeriya ta gargaɗi ‘yan ƙasar da ke shirin tafiya zuwa Australia kan tabarbarewar tsaro da ake samu a wasu biranen ƙasar.
A wata sanarwa da muƙaddashin mai magana da yawun ma’aikatar, Mista Kimiebi Imomotimi Ebienfa, ya ce rahotanni sun nuna cewa akwai yawaitar wariya, cin zarafi, da ƙyamar baƙi ‘yan ƙasashen waje, musamman Musulmai, a wasu sassan Australia.
- Rahoto: Sana’ar Watsa Labarai Ta Kasar Sin Ta Shiga Zamanin Cudanyar Digital Da Basira.
- NAHCON Ta Mayar Wa Alhazan Jihar Kaduna Kudaden Rangwame Na Aikin Hajjin 2023
Ya ƙara da cewa duk mai shirin tafiya ko mazauna ƙasar su yi taka-tsantsan domin guje wa faɗa wa hatsari.
A farkon watan Disamban 2024, an samu hare-hare a kan Musulmai da Yahudawa a wani yanki kusa da birnin Sydney, abin da ya ƙara tayar da hankali.
Sanarwar ta kuma zo sa’o’i bayan Australia ta gargaɗi ‘yan ƙasarta kan zuwa Nijeriya saboda matsalolin tsaro.
Ma’aikatar ta buƙaci ‘yan Nijeriya da ke Australia su sanar da ofishin jakadancin Nijeriya da ke Canberra idan sun fuskanci wani nau’in wariya ko musgunawa.
Ta kuma ja hankalin masu shirin tafiya su yi la’akari da wannan gargaɗi kafin tafiyarsu.