A halin yanzu gwamnatin tarayya ta sanar da samar da wani shiri na musamman da zai karfafa wa mata shiga harkokin hakar ma’adanai a sassan Nijeriya don a dama da su.
Ministan ma’adanai, Dakta Dele Alake, ya sanar da haka ranar Talata a yayin kaddamar da shirin a Abuja. Ya ce, ana sa ran shirin zai karfafa shigar mata harkar haka da sarrafa ma’adanai a fadin kasar nan.
- ‘Yan Mata Mu Yi Karatu Sannan Mu Kama Sana’a – Khadija Sambo
- Da Dumi-Dumi: ‘Yan Bindiga Sun Kashe Jami’an Tsaron Zamfara 3
Ya kara da cewa, shirin na hadin gwiwa ne tsakanin ma’aikatar ma’adanai da ma’akatar karafa tare da tallafin bankin duniya da wasu kungiyoyin bayar da tallafi na duniya.
”Dukkan ma’aikatun biyu mun tsayu na ganin wannan shirin ya samu gindin zama tare da samun nasarar da ake bukata, muna fatan ganin mata sun zama jagorori a bangarori da dama na haka da sarrafa ma’adanai a kasar nan,” in ji shi.
Dakta Alake ya kuma jaddada cewa, shugaban kasa Bola Tinubu ya dauki lamarin karfafa mata a dukkan bangarorin tafiyar da tattalin arzikin kasar na da matukar muhimmanci. Kuma ba zai lamunci wani ya yi wasa da shi ba.