Ministan Tsaro, Mohammed Abubakar Badaru, ya kaddamar da kwamitin aiwatar da ayyuka na mutane takwas domin samarwa da kuma sanya na’urorin sa ido kan hanyar Abuja zuwa Kaduna.
Ministan ya ce samar da hanyoyin tsaro na sa ido a hanyar Abuja zuwa Kaduna da na layin dogo zai magance kalubalen tsaro da ake yawan samu a kan hanyar.
Kwamitin dai zai tabbatar da kafa na’urorin sa ido da sauran ayyukan tsaro a hanyoyin biyu na kan titin Kaduna zuwa Abuja da na layin dogo cikin watanni 18.
Talla