Domin karfafa shirin fara amfani da motoci masu Iskar Gas a fadin kasar nan, gwamnatin tarayya ta kaddamar kwamiti na musamman da zai samar da motoci masu amfani da Iskar Gas da kuma tashoshin sayar da isakar gas din, kwamitin zai fara aiki ne a Jiihar Legas a karkashin jagorancin kwamitin shugaban kasa a kan amfani da Iskar Gas ’Presidential CNG Initiatibe (P-CNGi)’.
Shugaban kwamitin na kasa, Micheal Oluwagbemi, ya ce an kaddamar da tashoshin Iskar Gas din ne a fadin Nijeriya don ya zama wani mataki mai muhimmanci a hakoron da gwamnati take yi na tabbatar da an fara kaurace wa amfani da man fetur a motoci.
- Baje Kolin CIIE Na Kara Jan Hankalin Sassa Kasa Da Kasa
- Yadda Rakiyar Gwamnan Kano Ga Tagwayen da ke Manne Da Juna Ta Dauki Hankalin Al’umma
Ya kuma kara da cewa, cibiyar samar da Iskar Gas din da aka kaddamar zai taimakawa wajen samar da makashin da ba ya cutar da yanayi zai kuma jagoranci makomar tattalin arzikin kasa a nan gaba, an dai kaddamar da tashar ne a KM 42, a Lekki-Epe ta jihar Legas.
Idan za a iya tunawa an sanar da kafa tashoshin samar da Iskar Gas 7 a sassan Nijeriya.
Kwamitin ya kuma mika motoci da aka sauya su suka fara amfani da Iskar Gas ga fadar shugaban kasa da ke Abuja.