Gwamnatin Tarayya ta musunta labaran da ke yawo cewa, ta shiga tsakani kan tsare dan takarar shugaban kasa a jami’yyar LP, Peter Obi da aka yi a Birtaniya.
Leadership ta ruwaito cewa, an tsare Obi na dan wani lokaci a filin jirgin saman Hearthrow da ke a Landan bisa rashin gane ko shi waye bayan ya je kasar don gudanar da bikin Easter.
- Fyade: Abubuwan Da Ke Hadasawa, Illoli Da Yadda Za A Magance
- Shirin Kawo Karshen Yi Wa Mata Kaciya Nan Da 2030
A ranar Alhamis ne, wani hoton bogi ya karade kafafen sada zumunta, inda hoton ya nuna shugaban hukumar ‘yan Nijeriya mazauna kasar waje (NiDCOM) Hon. Abike Dabiri-Erewa zaune a wani ofis tare da Obi da kuma wani jami’in tsaro na Birtaniya domin neman karbar belin Obi.
Sai dai, mai shugaban sashen yada labarai kuma magana da yawun NiDCOM Abdur-Rahman Balogun, ya musunta labarin, inda ya ce shugabarsa Dabiri-Erewa ba ta je Birtaniya ba kuma ba ta hurumin neman belin kowane dan Nijeriya da ake zarginsa da aikata laifi a Birtaniya.
Shi ma Bashir Ahmad, hadimin shugaban kasa Muhammadu Buhari a sanarwar da ya wallafa a shafinsa na Tweeter a ranar Alhamis, ya nesanta gwamnatin tarayya kan neman belin Peter Obi kan tsare shin da jami’an tsaron suka yi a Birtaniya.