ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Wednesday, July 22, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Shirin Kawo Karshen Yi Wa Mata Kaciya Nan Da 2030

by Leadership Hausa
3 years ago
Mata

Kididdigar Majalisar Dinkin Duniya ta tabbatar da cewa, mata fiye miliyan 200 a fadin duniya suka fuskanci yi musu kaciya abin da ake kira da ‘Female Genital Mutilation’ (FGM) a turance.

Rahoto ya kuma nuna cewa a wannan shekarar ta 2023 akwai mata fiye da Miliyan 4.2 dake fuskantar yiwuwar a yi musu kaciyar.

  • Wane Irin Kuzarin Da Ke Addabar Kasuwancin Waje Na Kasar Sin?
  • Amurka Za Ta Iya Daidaita Batun Bazuwar Bayanan Sirri Kuwa?

Haka kuma majalisar ta kiyasata cewa, katsewar zuwa makaranta da mastalar cutar korona ta haifar zai iya jefa wasu matan fiye da miliyan 2 su fada komar masu yi wa mata kaciya a cikin shekaru masu zuwa in har ba a dauki matakin da ya kamata ba.

ADVERTISEMENT

Nijeriya ce kasa ta uku a duniya da ke tattare da mafi yawan mata a da aka taba yi wa kaciya, kamar yadda kungiyar majalisar dinkin duniya ta UNICEF ta bayyana a rahotonta. Hukumar ta kuma kara da cewa, yi wa mata kaciya yana kara karuwa a Nijeriya musamman a kan ‘yan mata masu shekaru 0 zuwa 14 a duniya. Abin takaicin kuma shi ne alkalumman ya tashi daga kashi 16.9 a shekarar 2013 zuwa kashi 19.2 a shekarar 2018, ‘‘Wannan abin damuwa ne matuka,”. UNICEF ta kuma bayyana cewa, mata fiye miliyan 68 a fadin duniya suke fuskantar yiwuwar a yi musu kaciya a tsakanin shekarar 2015 zuwa shekarar 2030.

A shekarar 2012, babban zauren majalisar dinkin duniya (UNGA) ya ayyana ranar 6 ga watan Fabrairu na duk shekara a mastayin ranar yekuwa da yaki da yi wa mata kaciya a duk duniya, ranar da za a kara jaddada aniyar yaki da wannan mummunan al’adar da kokarin kawar da ita gaba daya.

LABARAI MASU NASABA

Yadda Gano Ma’adanin ‘Lithium’ Zai Sauya Rayuwar Al’ummar Kudancin Kaduna

Zaben Fidda Gwani Da Ake Takaddama:APC Ta Dauki Matakan Kauce Wa Shari’o’in Kotu

Taken bikin na wannan shekarar shi ne “Hada Hannu Da Maza da Matasa Don Kawo Kareshen Yi Wa Mata Kaciya”. An kaddamar da shirin ne tare da hadin gwiwar UNFPA-UNICEF da hadadiyyar Kungiyar yaki da yi wa mata kaciya ta Duniya.

An kirkiro da shirin ne a shekarar 2022 don samar da gudummawar al’ummar duniya don kawar da yi wa mata kaciya a fadinn duniya nan da shekarar 2030. Abin jin dadi a nan shi ne wannan shiri yana da alaka da tsarin cimma muradun karni mai lamba na 5.3, wanda ke neman a kawo abubuwan da za su iya cutar da al’umma daga nan  zuwa shekarar 2030. Bangaren shirin ya bayar da karfi ne a kan kasashen da suka fi yawan wadanda ake ganin za a yi wa kaciyar a ‘yan shekaru masu zuwa.

Yi wa mata kaciya ya yi kamari a Nijeriya inda ake samun fiye da mata Miliyan 19.9 da aka yi wa kaciyar. Lamarin na Nijeriya yana kara kamari musammman a tsakanin mata masu shekara 15 zuwa 49 amma ya yi kasa daga kashi 25 a shekarar 2013 zuwa kashi 20 a shekarar 2018, binciken ya kuma nuna yadda lamarin ya kuma karu a tsakanin yara ‘yan shekara 0 zuwa 14 daga kashi 16.9 zuwa kashi 19.2 a daidai wannan lokacin da ake magana. An kuma gano cewa kashi 86 na matan da aka yi wa kaciyar ana yi musu ne a tsakanin shekara 5 yayin da kashi 8 kuma an yi musu ne a tsakanin shekara 5 zuwa 14.

Tuni wakilin kungiyar majalisar dinkin duniya ta UNICEF a Nijeriya, Peter Hawkins ya bayyana cewa, yi wa mata kaciya bashi da wani tasiri a bangaren lafiya. Bayani daga kafafaen yada labarai ya nuna cewa, an yi wa mata kaciyar ne a yankin kudu maso yammancin kasar nan in da ake da kashi 35 yayin da kuma ake da karancin wadanda ake yi wa kaciyar a yankin Arewa maso gabas inda suke da kashi 6 kacal.

Jihohi biyar da aka fi yi wa mata kaciya a Nijeriya sune: Ebonyi, Ekiti, Imo, Osun da Oyo. Inda fiye da ‘yan mata da mata Miliyan 3 suka samu kansu da kaciya a tsakanin shekara 5 kamar yadda kididdiga ya nuna a shekarar 2022.

Ana yi wa matan kaciyar ne a mastayin karya dokokin hakkinsu na yara da mata kamar yadda dokokin kare hakkin yara ya nuna, haka kuma karyar hakkinsu ne na abin da ya shafi sirrinsu da kuma hakkinsu na kasancewa cikin ‘yanci, hanyoyin da ke bi wajen yi wa matan kaciya yana kai wa ga mutuwar wasu a sassan Nijeriya.

Bayani daga wani littafi da wata sharariyar mai fafuftukar yaki da yi wa mata kaciya mai suna Frances A. Althaus, ta sanar da yadda a shekarar 1984 suka yi taron a garin Dakar ta kasar Senegal, inda suka tattauana lamarin yi wa mata kaciya da sauran miyagun al’adu da ke cutar da rayuwar mata a sassan Afrika, daga nan suka kafa wata karkaffar kwamitin wanda zai yi aikin wayar da kan al’umma aka wannan mummuna al’ada.

An kuma bayyani a cikin littafin inda aka bayyana yadda kwamitin ya jagoranci kafa rassan kwamitoci a kasashe fiye 20 a sassan Afirika sun kuma bayar da gaggarumin gudumawa wajen yaki da wannan mummunar al’adar na yi wa mata kaciya, sun bayar da karfi a kan bayyana irin yadda yi wa mata kaciya yake cutar da rayuwar mata, an kuma samu babbar nasara a wannan yakin. Wanna gwagwamaryar ya haifar da wasu kananan kungiyoyi da suka yi fice a yakin da aka fuskanta na yi wa mata kaciya, sun kuma hada da ‘NOW’ a Nijeriya da kuma ‘Mandalaeo Ya Wanawake’ a kasar Kenya da ‘New Woman’ a kasar Egypt.

Littafin ya kuma fito da nasarar da aka samu a babban taro karo na 4 da aka yi a kasa Chana a shekarar 1995 inda aka samu nasarar ta yadda taron ya ayyana haramci ga wannan al’aada na yi wa mata kaciya a duniya, an kuma ayyana al’adar a matsayin tarzoma ga mata kuma karya hakkinsu ne.

Haka kuma bincike ya nuna cewa, ana wannan al’ada na yi wa mata kaciya a wasu kasase na yankin Asiya da latin Amurka abin takaici kuma shi ne wasu ‘yan gudun hijira dake zaune a yankin Turai ta Yamma, Arewacin Amurka da kasar Australia da New Zealand suna ci gaba da yi wa yaransu mata kaciya a boye.

A yayin da ranar Majalisar Dinkin Duniya ta ware na yaki da yi wa mata kaciya yake kara karatowa, a mastayinmu na jarida muna kara kira ga gwamantin tarayya ta gaggauta sanya ido a kan wuraren da ake samun rahoton karuwar yi wa mata kaciya, bai kamata a tilastawa kowa fadawa irin wannan mummunan al’adar ba. Yakamata a samar da wata karkarfar kwamiti domin fadakar da al’umma a kan bukatar kawo karshen wannan mummunan al’ada. Yakamata mu hada hannu mu fattaki al’adar yi wa mata kaciya.

Mata
Leadership Hausa
Website |  + postsBio
  • Leadership Hausa
    Batun Yawan Bashin Da Nijeriya Ke Ciyowa Daga Ketare
  • Leadership Hausa
    Tallafa Wa Yara Masu Buƙatu Na Musamman Shi Ne Burina
  • Leadership Hausa
    Dole Mata Su Rungumi Sana’o’i Domin Tsira Daga Takaicin Zamani —Ramatu Bello
  • Leadership Hausa
    Batun Dakile Shan Taba Sigari A Tsakanin Yara A Nijeriya

MASU ALAKA

Yadda Gano Ma’adanin ‘Lithium’ Zai Sauya Rayuwar Al’ummar Kudancin Kaduna
Rahotonni

Yadda Gano Ma’adanin ‘Lithium’ Zai Sauya Rayuwar Al’ummar Kudancin Kaduna

July 18, 2026
Zaben Fidda Gwani Da Ake Takaddama:APC Ta Dauki Matakan Kauce Wa Shari’o’in Kotu
Rahotonni

Zaben Fidda Gwani Da Ake Takaddama:APC Ta Dauki Matakan Kauce Wa Shari’o’in Kotu

July 17, 2026
Wasu Sassan Birnin Abuja Na Fuskantar Barazanar Rusau
Rahotonni

Wasu Sassan Birnin Abuja Na Fuskantar Barazanar Rusau

July 17, 2026
Next Post
Dalilan Karuwar Hare-haren Ta’addanci Bayan Zaben 2023

Dalilan Karuwar Hare-haren Ta’addanci Bayan Zaben 2023

LABARAI MASU NASABA

Hisbah

Rajistar Shirin Auren Gata Na Kano Kyauta Ce, In Ji Hukumar Hisbah

July 22, 2026
An Karyata Maganar Wai Akwai “Matsin Kasar Sin”

An Karyata Maganar Wai Akwai “Matsin Kasar Sin”

July 22, 2026
Sojoji Sun Daƙile ‘Yan Ta’adda Daga Karɓar Haraji A Yobe

Sojoji Sun Daƙile ‘Yan Ta’adda Daga Karɓar Haraji A Yobe

July 22, 2026
Sojoji Sun Kashe ‘Yan Bindiga, Sun Ceto Mutane A Kaduna Da Filato

Sojoji Sun Daƙile Yunƙurin Garkuwa Da Mutane, Sun Ceto Wasu Da Aka Sace A Zamfara, Katsina Da Kebbi

July 22, 2026
NNPP Ta Yi Barazanar Maka INEC A Kotu Kan Ƙin Bin Umarnin Dawo Da Tambarinta A Kan Lokaci

NNPP Ta Yi Barazanar Maka INEC A Kotu Kan Ƙin Bin Umarnin Dawo Da Tambarinta A Kan Lokaci

July 22, 2026
Kwankwaso Zai Koma ADC Ranar Litinin

2027: Magoya Bayan Tinubu Sun Yi Watsi Da Sukar Takarar Musulmi-Musulmi Da Kwankwaso Ya Yi

July 22, 2026
Shugaban Laliga Ya Buƙaci Infantino Ya Sauka Daga Shugabancin FIFA

Shugaban Laliga Ya Buƙaci Infantino Ya Sauka Daga Shugabancin FIFA

July 22, 2026
Kasar Sin: Yunkurin Japan Na Kalubalantar Odar Kasa Da Kasa Bayan Yakin Duniya Na Biyu A Bayyana Yake Kasa

Kasar Sin: Yunkurin Japan Na Kalubalantar Odar Kasa Da Kasa Bayan Yakin Duniya Na Biyu A Bayyana Yake Kasa

July 21, 2026
Babban Jami’in Diflomasiyyar Sin Ya Jaddada Matsayar Dangantakar Kasar Da Turai Ta Hadin Gwiwa

Babban Jami’in Diflomasiyyar Sin Ya Jaddada Matsayar Dangantakar Kasar Da Turai Ta Hadin Gwiwa

July 21, 2026
Yayin Da Na’ura Ta Fara Tunani: Bil’adama Ne Kadai Zai Iya Tunkarar Lamarinta

Yayin Da Na’ura Ta Fara Tunani: Bil’adama Ne Kadai Zai Iya Tunkarar Lamarinta

July 21, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.