Gwamnatin Tarayya ta sanar cewa Samun Lambar Tantance Haraji (Tax ID) zai zama wajibi ga duk ƴan Nijeriya da ke hulɗa da bankuna da sauran ayyukan hada-hadar kuɗi daga ranar 1 ga Janairu, 2026.
Wannan sabon umarni yana cikin Dokar Gudanar da Haraji ta Nijeriya, 2025, wacce shugaban ƙasa Bola Tinubu ya rattaba hannu kwanan nan. A ƙarkashin Sashe na II, ɓangare na 4 na dokar, dukkan mutane da ƙungiyoyi da abin da haraji ya shafa dole ne su yi rajista a hukumomin haraji da suka dace kuma su samu Katin Tantance Haraji (Tax payer Identification Card).
- Ƙungiyar Ƙwadago Ta Ba Gwamnati Wa’adin Kwana 14 Ta Janye Sabon Harajin Man Fetur
- Shugaban Ghana: Manufar Soke Biyan Harajin Kwastam Ta Kasar Sin Ta Ba Da Damammaki Ga Afirka
Dokar ta ƙara ƙayyade cAewa kowace ma’aikata, sashen gwamnati, da hukumar a matakin tarayya, jiha, ko ƙaramar hukuma dole ne su samu Lambar Tantance Haraji (Tax ID). Haka kuma, waɗanda ba mazauna Nijeriya ba ko ƙungiyoyi masu samar da kaya ko ayyuka masu haraji a ƙasar dole ne su samu wannan lambar.
Dokar ta ba hukumomin haraji ikon bayar da Tax ID a madadin waɗanda suka gaza yin rajista, ko su ƙi karɓar buƙata idan bayanan da ake da su sun nuna hakan ya dace. Dole ne a sanar da mai nema duk wata cikin kwanaki biyar na aiki.
Bugu da ƙari, Sashe na 8 na dokar ya sanya mallakar Tax ID sharaɗi ne kafin shiga kwangilolin gwamnati, mu’amaloli na banki, inshora, kasuwar hannayen jari, da sauran ayyukan kuɗi.
Dokar ta ba da damar dakatarwa na ɗan lokaci ko kuma cire rajistar Tax ID gaba ɗaya idan mai riƙe da shi ya daina gudanar da kasuwanci.
A gefe guda, Dokar Kafa Hukumar Haraji ta Nijeriya, 2025, ta ba Shugaban Zartarwa na Hukumar babban ikon, wanda zai kasance shugaban Kwamitin Gudanarwa na hukumar. Kwamitin zai haɗa da wakilai daga Ma’aikatan Kuɗi, Tsare-Tsaren Ƙasa, Shari’a, Man Fetur, Babban Bankin Nijeriya, Haraji da Kwastam, Hukumar Kula da Harkokin Kamfanoni, da sauran muhimman hukumomi.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp