Ministan tsaro, Mohammed Abubakar, a daren ranar Alhamis ya sake jaddada aniyar gwamnatin tarayya na magance matsalar ‘yan bindiga da kuma rashin tsaro a fadin Nijeriya baki daya.
Ministan ya bayyana haka ne a lokacin da ya kai wa Gwamna Uba Sani ziyara a gidan gwamnatin Sir Kashim Ibrahim da ke Kaduna a wani rangadin da ya ke yi a shiyyar Arewa maso Yamma.
- An Yi Bikin Murnar Cika Shekaru 20 Da Kafa Cikakkiyar Dangantakar Abokantaka Bisa Manyan Tsare-tsare Tsakanin Sin Da Italiya A Milan
- A Farfado Da Rayuwar Wadanda Ambaliyar Ruwa Ta Shafa A Maiduguri
Ziyarar dai na da nufin kammala shirye-shiryen kaddamar da shirin ‘Operation Fansar Yamma,’ rundunar hadin gwiwa ta rundunar soji da aka kafa domin magance matsalar rashin tsaro a yankin.
Abubakar, a lokacin da yake zantawa da manema labarai jim kadan bayan kammala ziyarar, ya jaddada kafa cibiyar gudanarwar tsaro a shiyyar Arewa maso Yamma a matsayin wani muhimmin mataki na magance matsalar ‘yan bindiga da suka addabi yankin.
Ministan ya kuma bayyana irin kokarin da gwamnatin kasar ke yi na hadin gwiwa da kasashe makwabta musamman jamhuriyar Nijar wajen yaki da ta’addanci da safarar makamai.
A nasa jawabin, a lokacin da yake maraba da Ministan, Gwamna Sani ya jaddada bukatar hadin kan shugabannin yankin domin magance matsalar rashin tsaro.
Gwamna Sani ya nuna godiya ga gwamnatin tarayya bisa jajircewar da ta yi na ganin ta magance matsalolin rashin tsaro da ke addabar shiyyar Arewa maso Yamma.
Ya kuma bayyana damuwarsa kan illar rashin tsaro a shiyyar Arewa maso Yamma, da suka hada da karancin abinci, karancin hanyoyin kiwon lafiya, da karuwar talauci.
Sai dai gwamnan ya bayyana fatansa na cewa, shirin “Operation Fansar Yamma” wanda ake shirin kaddamarwa, zai samar da yanayin zuba jari da bunkasar tattalin arziki a yankin.
Gwamnan ya kuma bayar da shawarar mayar da ‘Operation Safe Haven’ da ke Kudancin Kaduna zuwa shiyya ta 1 da ke Kaduna maimakon shiyya ta uku da ke Jos a Jihar Filato domin samun saukin gudanar da ayyuka.
Ya yaba da goyon bayan da shugaban kasa Bola Tinubu ke yi bai wa shiyyar Arewa maso Yamma, ya kuma nuna godiya ga Ministan Tsaro, Shugaban Hafsan Tsaro, da Babban Hafsan Soja bisa goyon bayan da suke bai wa yankin.