Gwamnatin Tarayya ta soke faretin da aka shirya yi don bikin cikar Nijeriya shekara 65 da samun ’yancin kai a ranar Laraba, 1 ga watan Oktoba, 2025.
A wata sanarwa daga Ofishin Sakataren Gwamnatin Tarayya, ya ce an ce sokewar ba ta za ta rage muhimmancin wannan rana ba.
- Kasashen Sin Da Afrika Za Su Hada Kai A Bangaren Intanet
- Dole Arewa Ta Yi Magana Da Murya Ɗaya Kan Tsaro Da Tattalin Arziki, In ji Gwamnan Zamfara
Segun Imohiosen, Daraktan Hulɗa da Jama’a, ya ce sauran shirye-shiryen bikin za su gudana kamar yadda aka tsara.
Gwamnati ta nemi afuwa kan duk wata matsala da wannan mataki zai iya jawo wa ’yan ƙasa.
Haka kuma ta roƙi ’yan Nijeriya su ci gaba da goyon bayan tsare-tsaren Shugaba Bola Tinubu, tana mai tabbatar da cewa gwamnati na ƙoƙarin gina Nijeriya.