Ministan ma’aikatar ma’adinai, Oladele Alake, ya sanar da soke lasisin hakar ma’adinai a wurare 1,633 tare da gargadin kamfanonin da su gaggauta ficewa daga wurin.
A cewarsa, jami’an tsaro tare da hadin guiwar hukumar kula da ma’adinai ta ma’aikatar, an ba su izinin kamo duk wanda aka samu da laifin karya dokar.
- Guterres Ya Jinjinawa Sin Game Da Shirya Muhawara Kan Tasirin Samar Da Ci Gaba Mai Dorewa
- Harin Boko Haram: Mataimakin Gwamnan Yobe Ya Ziyarci Wadanda Suka Jikkata A Asibiti
Da yake magana a wani taron manema labarai a Abuja a yammacin ranar Talata, Alake ya bayyana cewa, an soke lasisin hakar ma’adinan ne saboda rashin biyan harajin shekara da aka kayyade akan lokaci.
Ya ce, duk da lamunin kwanaki 30 da ofishin ma’adinai na Cadastre ya bayar, amma kamfanonin sun ki biyan hakkin gwamnati da ya rataya akansu.