Gwamnatin tarayya ta tabbatar da ɓullar cutar murar tsuntsaye a jihar Kano, wadda tafi shafar Agwagi, Talotalo da kajin leyas.
A wata takardar da Dr. Taiwo Olasoju ya fitar a madadin babban jami’in kula da lafiyar dabbobi na Nijeriya a ranar Talata, gwamnatin ta nuna damuwa kan yadda cutar ke kara yaduwa musamman a wannan kakar.
Sanarwar ta bukaci ofisoshin kula da dabbobi na jihohi da hukumomin da abin ya shafa da su kara sa ido tare da aiwatar da tsauraran matakan kariya daga kamuwa da cutar.
Hukumar ta kuma ba da shawarar aiwatar da gangamin wayar da kan jama’a don ganowa da magance sabbin nau’ukan cutar cikin gaggawa.
Ya tabbatar da cewa, samfurori da aka aika don gwaji sun tabbatar da bullar kwayar cutar a cikin makon farko na Janairun 2025.
Sai dai, ba a sami rahoton bullar cutar ba a gidajen kiwon kaji na kasuwanci ba, wanda hakan, taimako ne matuka ga masu kiwon kaji.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp