Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima, ya ce Gwamnatin Tarayya za ta shuka itatuwan dabino miliyan 100 a faɗin ƙasar nan tare da farfaɗo da harkar noman kaka.
Ya bayyana hakan ne a wani taron tallafa wa ƙananan ‘yan kasuwa da aka gudanar a Jihar Ondo.
- Kwamishinan Sufuri Ya Yi Murabus Kan Belin Wani Da Ake Zargi Da Laifin Safarar Kwaya A Kano
- Hare-haren Boko Haram Da ‘Yan Bindiga Ya Ragu A Cikin Shekaru Biyu – Ribadu
Shettima ya ce ƙananan sana’o’i suna da matuƙar muhimmanci domin suna samar da kashi 90 na ayyukan yi a Nijeriya kuma suna rage talauci.
Ya kuma bayyana cewa ƙananan ‘yan kasuwa 65 daga Ondo sun samu tallafi daga cikin kuɗin Naira biliyan 75 da Gwamnatin Tarayya ta ware.
Shugabannin da suka halarci taron, ciki har da Gwamnonin Ondo da Ekiti da kuma Ooni na Ife, sun buƙaci ‘yan Nijeriya da su riƙa sayen kayan da aka sarrafa a cikin gida domin bunƙasa tattalin arziƙi.