Gwamnatin Tarayya za ta miƙa aikin gina titin Koko-Mahuta-Dabai-Zuru mai nisan kilomita 87 ga Gwamnatin Jihar Kebbi.
Aikin, wanda aka ba da kwangilar shi tun Disambar 2020 kan kuɗi Naira biliyan 19.7, an samu kammala kilomita biyar kacal cikin shekaru huɗu sakamakon matsalar kuɗaɗe da wasu kalubale.
- NAPTIP Ta Kuɓutar Da Yara 19 Da Aka Sace A Kebbi
- Gwamnatin Kebbi Ta Kafa Kwamitin Kwato Kuɗaɗen Da Aka Sace A Asusun Marayun Jihar
A yayin ziyarar duba aikin tare da haɗin gwuiwa, Mr. Ishaya Vandi-Joseph, shugaban Aiyukan Gine-gine na Jihar Kebbi, ya bayyana cewa gwamnatin Kebbi ta bi doka wajen karɓar aikin don tabbatar da saurin kammala shi.
Gwamna Nasir Idris, wanda kakakin Majalisar Dokoki Muhammad Usman-Zuru ya wakilta, ya tabbatar da cewa jihar za ta tabbatar da kammala aikin cikin ingancin.
Wannan hanya tana da matukar muhimmanci ga sassa bakwai na ƙananan hukumomin Jihar, musamman don bunƙasa harkokin noma a jihar.