Ministan lafiya da walwalar jama’a, Farfesa Muhammed Ali Pate, ya bayyana cewa, nan ba da dadewa ba shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu zai rattaba hannu kan wata doka domin rage tsadar magunguna da kayayyakin kiwon lafiya.
Ministan ya bayyana haka ne a ranar Laraba a wani taron manema labarai na ministoci wanda ministan yada labarai da wayar da kan jama’a, Mista Mohammed Idris, ke jagoranta a Abuja.
- Mazauna Yankunan Karkarar Sin Sun Samu Karin Kyautatuwar Rayuwa
- Gwamnatin Tarayya Za Ta Samar Da Cibiyoyin Koyon Sana’o’i Fiye Da 24
Yayin da yake bayyana irin gagarumin ci gaban da aka samu a fannin kiwon lafiya karkashin gwamnatin shugaba Ahmed Bola Tinubu tun daga watan Mayun shekarar 2023, Pate ya ce, duk da ficewar da manyan kamfanonin magunguna na duniya suka yi daga kasar, gwamnati ta dukufa wajen rage tsadar magunguna da kayayyakin kiwon lafiya a kasar nan.
Ya ce, “wata doka ta Shugaba Tinubu na nan tafe don rage tsadar magunguna da kayayyakin kiwon lafiya a kasar nan.”