• English
  • Business News
Saturday, July 26, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Gwamnatin Tinubu Ba Za Ta Goyi Bayan Auren Jinsi Ba – Minista 

by Sulaiman
1 year ago
in Labarai
0
Yajin aiki
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsAppTelegram

Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kai, Alhaji Mohammed Idris, ya bayyana cewa gwamnatin Bola Ahmed Tinubu ba za ta goyi bayan duk wani yunƙuri na auren jinsi ko tarayyar ‘yan luwaɗi da maɗigo a Nijeriya ba.

Ministan ya bayyana haka ne a yayin da yake martani kan labarin da aka yaɗa a ranar Alhamis cewa Gwamnatin Tarayya ta rattaba hannu kan wata yarjejeniya da aka yi a ƙasar Samoa, wadda za ta ba da dama a hukumance ga ‘yan luwaɗi da masu maɗigo a Nijeriya.

  • Huldar Abotar Dindindin Tsakanin Sin Da Kazakhstan Na Samun Ci Gaba Zuwa Sabon Mataki
  • An Fitar Da Alkaluman Awon Yadda Ake Hade Ayyukan Masana’antu Da Fasahar AI A Sin

A rahoton da wasu kafafen yaɗa labarai suka buga, an ruwaito cewa, yarjejeniyar ta ƙunshi wasu tanade-tanade ne waɗanda ke buƙatar goyon bayan kare haƙƙin ‘yan luwaɗi da masu maɗigo a matsayin sharaɗin samun tallafin kuɗi da sauran taimako daga ƙasashen da suka ci gaba.

Lamarin dai ya haifar da ce-ce-ku-ce, inda wasu malaman addini da masu rajin kare haƙƙin ɗan Adam ke sukar gwamnati kan amincewa da yarjejeniyar da ta yi.

To amma a ƙarin hasken da ya yi kan yarjejeniyar, Minista Idris ya ce ai Nijeriya tana da dokoki tun tuni waɗanda suka haramta auren jinsi ko tarayyar ‘yan luwaɗi da masu maɗigo, kuma dokokin sun girmi wannan yarjejeniyar ta Samoa da ake ta ce-ce-ku-ce a kan ta.

Labarai Masu Nasaba

Dangote Ya Ajiye Muƙamin Shugabancin Kamfaninsa Na Siminti

Rayuwar Aso Rock: Shugabannin Nijeriya 4 Da Suka Mutu Bayan Kammala Wa’adin Mulki

Ya ce, “A ranar 28 ga Yuni, 2024 ne gwamnatin Nijeriya ta rattaba hannu kan yarjejeniyar Samoa ɗin a sakatariyar Ƙungiyar Ƙasashen Afirka, Karibbiyan da Pacific (OACPS) a birnin Brussels na ƙasar Beljiyam.

“An fara tattaunawa kan yarjejeniyar tun a shekarar 2018, a lokacin taron Majalisar Ɗinkin Duniya karo na 73. Ɗaukacin ƙasashe membobin Tarayyar Turai su 27 da ƙasashe 47 daga cikin 79 na OACPS ne suka rattaba hannu kan yarjejeniyar a garin Apia da ke Tsibirin Samoa a ranar 15 ga Nuwamba, 2018.

“Nijeriya ta rattaba hannu kan yarjejeniyar ne a ranar Juma’a, 28 ga Yuni, 2024. Hakan ya biyo bayan nazarin da ta yi tare da tuntuɓar Kwamitin Ministoci da Ma’aikatar Kasafin Kuɗi da Tsare-tsaren Tattalin Arziki ta kafa tare da haɗin gwiwar Ma’aikatar Harkokin Ƙasashen Waje da Ma’aikatar Shari’a ta Tarayya.

“An tabbatar da cewa babu ɗaya daga cikin Tanade-tanade 103 na yarjejeniyar waɗanda suka saɓa wa Kundin Tsarin Mulki na 1999 wanda aka yi wa kwaskwarima ko dokokin Nijeriya, da sauran wasu dokoki.

“Bugu da ƙari, amincewar da Nijeriya ta yi yana ƙunshe da sanarwa mai ɗauke da kwanan wata 26 ga Yuni, 2024, inda ta fayyace fahimtar ta da kuma yanayin yarjejeniyar a ƙarƙashin ikon ta na cewa ba a amince da duk wani tanadi da ya saɓa wa dokokin Nijeriya ba.

“Yana da kyau a lura da cewa akwai dokar da aka kafa a Nijeriya game da dangantakar auren jinsi ɗaya tun a cikin 2014.”

A ƙarshe, ministan ya ce, “Ya zama wajibi a tabbatar wa da ‘yan Nijeriya cewa gwamnatin Shugaba Bola Tinubu, kasancewar ta gwamnati mai bin ƙa’ida, ba za ta shiga wata yarjejeniya ta ƙasa da ƙasa wadda za ta cutar da ƙasa da ‘yan ƙasar ta ba.

“Yarjejeniyar Samoa ba komai ba ce illa wani muhimmin tsarin doka na haɗin gwiwa tsakanin ƙasashen ƙungiyar OACPS da Tarayyar Turai don inganta cigaba mai ɗorewa, da yaƙi da sauyin yanayi da illolinsa, da samar da damar zuba jari, da samar da haɗin gwiwa tsakanin ƙasashe mambobin OACPS a matakin ƙasa da ƙasa.”

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

Tags: LuwadiMaɗigoSamoaTarayyar Turai
ShareTweetSendShare
Previous Post

Fifikon Manzon Allah (SAW): Darasi Daga Suratun Najmi (1)

Next Post

An Aike Ɗan Shekara 67 Gidan Yari Kan Zargin Yi Wa ‘Yan Mata 2 Fyaɗe Yana Ba Su ₦500 A Bauchi

Related

Dangote Ya Sake Zama Wanda Ya Fi Kowa Kudi A Afrika Karo Na 12
Manyan Labarai

Dangote Ya Ajiye Muƙamin Shugabancin Kamfaninsa Na Siminti

5 hours ago
Rayuwar Aso Rock: Shugabannin Nijeriya 4 Da Suka Mutu Bayan Kammala Wa’adin Mulki
Rahotonni

Rayuwar Aso Rock: Shugabannin Nijeriya 4 Da Suka Mutu Bayan Kammala Wa’adin Mulki

7 hours ago
Gwamnan Jigawa Ya Rattaba Hannu Kan Kudirin Dokar Tabbatar Da Hisbah
Labarai

Gwamnan Jigawa Ya Rattaba Hannu Kan Kudirin Dokar Tabbatar Da Hisbah

8 hours ago
Jihohin Da Ke Shirin Rage Kudin Wutar Lantarki Su Shirya Biyan Tallafi – Ministan Wuta
Labarai

Jihohin Da Ke Shirin Rage Kudin Wutar Lantarki Su Shirya Biyan Tallafi – Ministan Wuta

9 hours ago
majalisar kasa
Labarai

‘Yan Majalisa Sun Zargi Hukumomin Gwamnati Da Wawure Sama Da Naira Biliyan 103.8

10 hours ago
Majalisar Wakilai Ta Nemi Amurka Ta Maido Da Bizar Shekara Biyar Ga ‘Yan Nijeriya
Labarai

Majalisar Wakilai Ta Nemi Amurka Ta Maido Da Bizar Shekara Biyar Ga ‘Yan Nijeriya

11 hours ago
Next Post
An Aike Ɗan Shekara 67 Gidan Yari Kan Zargin Yi Wa ‘Yan Mata 2 Fyaɗe Yana Ba Su ₦500 A Bauchi

An Aike Ɗan Shekara 67 Gidan Yari Kan Zargin Yi Wa 'Yan Mata 2 Fyaɗe Yana Ba Su ₦500 A Bauchi

LABARAI MASU NASABA

Sin Da EU Suna Kokarin Samun Moriyar Juna A Shekaru 50 Masu Zuwa

Sin Da EU Suna Kokarin Samun Moriyar Juna A Shekaru 50 Masu Zuwa

July 25, 2025
Dalilin Da Ya Sa Har Yanzu Obi Da El-Rufai Ba Su Shiga ADC A Hukumance Ba — Kakakin Jam’iyyar 

Dalilin Da Ya Sa Har Yanzu Obi Da El-Rufai Ba Su Shiga ADC A Hukumance Ba — Kakakin Jam’iyyar 

July 25, 2025
Dangote Ya Sake Zama Wanda Ya Fi Kowa Kudi A Afrika Karo Na 12

Dangote Ya Ajiye Muƙamin Shugabancin Kamfaninsa Na Siminti

July 25, 2025
Binciken Jin Raayoyi Na CGTN: Duniya Ta Saba Da “Kauracewar” Amurka

Binciken Jin Raayoyi Na CGTN: Duniya Ta Saba Da “Kauracewar” Amurka

July 25, 2025
Jam’iyyar PDP Ta Janye Daga Shiga Zaɓen Ƙananan Hukumomi A Kebbi

2027: Masu Neman Takarar Shugaban Kasa A PDP Sun Kara Matsa Kaimi Bayan Ficewar Atiku

July 25, 2025
Xi Jinping Ya Karbi Takardun Nadi Daga Sabbin Jakadun Kasashen Waje

Xi Jinping Ya Karbi Takardun Nadi Daga Sabbin Jakadun Kasashen Waje

July 25, 2025
Rayuwar Aso Rock: Shugabannin Nijeriya 4 Da Suka Mutu Bayan Kammala Wa’adin Mulki

Rayuwar Aso Rock: Shugabannin Nijeriya 4 Da Suka Mutu Bayan Kammala Wa’adin Mulki

July 25, 2025
Wakilin Sin Ya Karyata Amurka Game Da Batun Yankin Xinjiang Na Sin a Taron Kwamitin Sulhun MDD

Wakilin Sin Ya Karyata Amurka Game Da Batun Yankin Xinjiang Na Sin a Taron Kwamitin Sulhun MDD

July 25, 2025
Gwamnan Jigawa Ya Rattaba Hannu Kan Kudirin Dokar Tabbatar Da Hisbah

Gwamnan Jigawa Ya Rattaba Hannu Kan Kudirin Dokar Tabbatar Da Hisbah

July 25, 2025
Kamfanin Sinotruk Na Kasar Sin Ya Kaddamar Da Sabbin Motocin Dakon Kaya A Kenya

Kamfanin Sinotruk Na Kasar Sin Ya Kaddamar Da Sabbin Motocin Dakon Kaya A Kenya

July 25, 2025
Talla

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In

Add New Playlist

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.