Jam’iyyar adawa ta PDP, ta soki gwamnatin Shugaba Bola Tinubu, inda ta ce tana cutar da ’yan Nijeriya.
PDP ta kuma ce jam’iyyar mai mulki ta APC, ta ci amanar ’yan ƙasa kuma za a kore ta a zaɓen shekarar 2027.
- PSC Ta Amince Da Ɗaga Darajar Jami’an ‘Yan Sanda 12 Daga Matakin CP Zuwa AIG, Da Sauransu
- Shirin Ba Da Horo A Kasar Sin Ya Taimaka Wa Inganta Masana’antar Gyadar Senegal
Sakataren Yaɗa Labarai na PDP na ƙasa, Debo Ologunagba, ne ya faɗi haka a wata tattaunawa da manema labarai a Abuja, ranar Litinin.
Ologunagba ya ce PDP na gyara tsarin cikin jam’iyyar domin ta kawo wa ’yan Nijeriya ingantacciyar madogara a zaɓen 2027.
A cewarsa, gwamnatin APC ta jefa ƙasar cikin mawuyacin hali na tattalin arziƙi, ta ƙara rashin tsaro da kuma jefa mutane cikin damuwa.
Ya ce PDP ce kaɗai ke da ƙarfin gina ƙasa.
“Wannan gwamnati ce da ke cewa mutane su yi azumi alhali su suna cin abinci sannan suna jin daɗi. Babu ɗan Nijeriya mai kishin ƙasa ko wata jam’iyya mai jin zafin halin da mutane ke ciki da za ta goyi bayan Tinubu a 2027. Gwamnatinsa kasuwanci ne mara riba,” in ji Ologunagba.
Kakakin PDP ya kuma nuna damuwa kan halin rashin tsaro, inda ya ambaci kisan gillar da aka yi wa mutane a Jihar Filato da kuma hari kan ɗan takarar PDP daga Anambra a Abuja, a matsayin alamu cewa rashin tsaro ya zama ruwan dare.
Ya ce ƙarfin PDP yana hannun talakawa, ba sai da manyan ’yan siyasa ba.
“Karfinmu yana hannun jama’a. Ko da wasu manya sun fice daga jam’iyya, talakawa suna tare da mu.”
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp