ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Thursday, November 13, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Gwamnatin Tinubu Ta Ba ‘Yan Jarida Cikakken ‘Yanci – Minista

by Sulaiman
2 years ago
Tinubu

Ministan Yaɗa Labarai Da Wayar Da Kai, Alhaji Mohammed Idris, ya tabbatar da cewa babu wani ɗan jarida ɗaya da aka kama ko aka ɗaure a ƙarƙashin gwamnatin Tinubu saboda gudanar da aikin jarida yadda ya kamata.

Ya jaddada cewa kafafen yaɗa labarai suna da cikakken ‘yanci a Nijeriya.

  • Hanyoyin Da Za A Taimaka Wa Malamai Inganta Aikinsu (6)
  • Yadda Za Ki Ja Hankalin Miji A Lokacin Da Ba Shi Da Sha’awa

Idris ya faɗi haka ne a yayin da ya ke amsa wata tambaya a wani taron manema labarai da ma’aikatar sa ta shirya tare da haɗin gwiwar Ma’aikatar Kula Da Muhalli ta Tarayya da kuma Hukumar Ilimi da Kimiyya ta Majalisar Ɗinkin Duniya (UNESCO), domin tunawa da Ranar ‘Yancin ‘Yan Jarida ta Duniya ta bana wanda aka yi a Abuja ranar Juma’a.

ADVERTISEMENT

Ya ce: “A zamanin wannan gwamnatin, a misali, ban ga wani mutum wanda aka ɗaure ko kuma ya yi gudun hijira sakamakon ‘yancin aikin jarida ba.

“Mun san abin da ya faru a ƙasar nan a baya. A wasu shekarun da suka gabata, mun san cewa dole ne ku bar ƙasar nan don samun damar ba da rahoto. Zan iya gaya muku cewa ‘yan jarida a Nijeriya suna da ‘yanci amma za a iya ƙarfafa ‘yancin ne idan aka tabbatar da gaskiya ta hanyar da muke kawo rahoto.”

LABARAI MASU NASABA

NDLEA Ta Ƙona Miyagun Ƙwayoyi Sama Da Kilo 52,000 A Kaduna

Jiga Jigan APC Sun Ziyarci Majalisar Wakilai Bayan Sauya Sheƙar Ƴan NNPP 2

Ministan ya ce Shugaban Ƙasa Tinubu ya fahimci muhimmancin yaɗa labarai yadda ya kamata wajen wayar da kai, faɗakarwa, da ilimantar da ‘yan Nijeriya da duniya baki ɗaya, inda ya ƙara da cewa ta hanyar ba da sahihan bayanai a kan lokaci za a iya faɗakar da kowa sosai, kuma kafafen yaɗa labarai na iya zama makami mai ƙima na bunƙasa gaskiya da riƙon amana.

“A matsayin mu na Ma’aikata da Gwamnati, mun ba da dama ga ‘yan jarida ba tare da wata matsala ba kuma mun samar da yanayi mai dacewa wanda ya ci gaba da ƙarfafa wa kafafen yaɗa labarai na Nijeriya ƙwarin gwiwa don bunƙasa,” inji shi.

Ministan ya tunatar da kafafen yaɗa labarai cewa yaɗa labarin ƙarya bai dace da aikin jarida ba kuma ba za a iya kwatanta shi da ‘yancin jarida ba.

Ya ce yayin da Shugaba Tinubu ke ƙoƙarin ganin Nijeriya ta zama wata ƙasa mai jan hankali wajen zuba jari kai-tsaye daga ƙasashen waje, dole ne kafafen yaɗa labarai su gabatar da kyakkyawan bayanin ƙasar ga ƙasashen duniya.

Yayin da ya ke magana kan taken Ranar ‘Yancin ‘Yan Jarida ta Duniya na bana, wato ”Jarida ta Duniya: Aikin Jarida a yayin da ake fuskantar Matsalar Muhalli,” Idris ya ce duniya na fuskantar matsalar muhalli mai girman gaske wanda ba a taɓa ganin irin sa ba, wanda ke haifar da barazana ba kawai ga duniya ba amma ga makomar bil’adama.

Ya ce sauyin yanayi, asarar rabe-raben halittu, gurɓacewar yanayi, da ƙarewar albarkatu munanan abubuwa ne da ke buƙatar ɗaukar matakin gaggawa kan wayar da kan jama’a.

Ya ce, “Mu yi imani da cewa ‘yancin ‘yan jarida ba wai kawai haƙƙin ɗan’adam ba ne; ya na da muhimmanci don ɗorewar muhalli. Idan babu ‘yan jarida masu ‘yanci da zaman kan su, ba za mu iya fatan magance matsalolin muhalli da mu ke fuskanta ba.

“Yaɗa labaran ƙarya yana lalata fahimtar jama’a game da matsalolin muhalli kuma yana hana mu damar ɗaukar matakai masu ma’ana.

“Don haka dole ne mu tsaya tsayin daka wajen kare ‘yancin ‘yan jarida tare da tallafa wa ayyukan ‘yan jarida masu sadaukar da kai wajen bayar da labarin gaskiya.”

Taron ya samu halartar Ƙaramin Ministan Kula da Muhalli, Dakta Iziaq Adekunle Salako; Mai ba Shugaban Ƙasa Shawara na Musamman kan Yaɗa Labarai da Dabaru, Mista Bayo Onanuga; Babbar Sakatariyar Ma’aikatar Watsa Labarai Da Wayar Da Kai, Dakta Ngozi Onwudiwe; Shugaban Ofishin UNESCO na Abuja, Mista Abdourahamane Diallo, da shugabannin hukumomin Ma’aikatar Yaɗa Labarai Da Wayar Da Kai da kuma Ma’aikatar Kula da Muhalli.

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

NDLEA Ta Ƙona Miyagun Ƙwayoyi Sama Da Kilo 52,000 A Kaduna
Labarai

NDLEA Ta Ƙona Miyagun Ƙwayoyi Sama Da Kilo 52,000 A Kaduna

November 13, 2025
Jiga Jigan APC Sun Ziyarci Majalisar Wakilai Bayan Sauya Sheƙar Ƴan NNPP 2
Manyan Labarai

Jiga Jigan APC Sun Ziyarci Majalisar Wakilai Bayan Sauya Sheƙar Ƴan NNPP 2

November 13, 2025
NIQS Ta Buƙaci Gwamnati Ta Tsawatar Kan Tsadar Gidajen Haya A Manyan Birane
Labarai

NIQS Ta Buƙaci Gwamnati Ta Tsawatar Kan Tsadar Gidajen Haya A Manyan Birane

November 13, 2025
Next Post
Idan Mace Ta Yi Barin Cikin Wata Biyu, Za Ta Dakatar Da Yin Sallah?

Idan Mace Ta Yi Barin Cikin Wata Biyu, Za Ta Dakatar Da Yin Sallah?

LABARAI MASU NASABA

Shugabannin Sin Da Comoros Sun Taya Juna Murnar Cika Shekaru 50 Da Kafa Alakar Diplomasiyya Tsakanin Kasashensu 

Shugabannin Sin Da Comoros Sun Taya Juna Murnar Cika Shekaru 50 Da Kafa Alakar Diplomasiyya Tsakanin Kasashensu 

November 13, 2025
Sanarwar Taron Ministocin Harkokin Waje Na Kungiyar G7 Ba Ta Da Tushe

Sanarwar Taron Ministocin Harkokin Waje Na Kungiyar G7 Ba Ta Da Tushe

November 13, 2025
NDLEA Ta Ƙona Miyagun Ƙwayoyi Sama Da Kilo 52,000 A Kaduna

NDLEA Ta Ƙona Miyagun Ƙwayoyi Sama Da Kilo 52,000 A Kaduna

November 13, 2025
An Kafa Cibiyar Kiwon Lafiya Ta Hadin Gwiwa Ta Farko Tsakanin Sin Da Afirka A Guinea

An Kafa Cibiyar Kiwon Lafiya Ta Hadin Gwiwa Ta Farko Tsakanin Sin Da Afirka A Guinea

November 13, 2025
Jiga Jigan APC Sun Ziyarci Majalisar Wakilai Bayan Sauya Sheƙar Ƴan NNPP 2

Jiga Jigan APC Sun Ziyarci Majalisar Wakilai Bayan Sauya Sheƙar Ƴan NNPP 2

November 13, 2025
NIQS Ta Buƙaci Gwamnati Ta Tsawatar Kan Tsadar Gidajen Haya A Manyan Birane

NIQS Ta Buƙaci Gwamnati Ta Tsawatar Kan Tsadar Gidajen Haya A Manyan Birane

November 13, 2025
Dalilai 5 Da Suka Jefa Ƙungiyar Ƙwallon Ƙafa Ta Kano Pillars Cikin Matsaloli A Kakar Wasa Ta 2024/25

Dalilai 5 Da Suka Jefa Ƙungiyar Ƙwallon Ƙafa Ta Kano Pillars Cikin Matsaloli A Kakar Wasa Ta 2024/25

November 13, 2025
Sau Ɗaya Na Taɓa Da-nasanin Fitowa A Cikin Fim – Tanimu Akawu

Sau Ɗaya Na Taɓa Da-nasanin Fitowa A Cikin Fim – Tanimu Akawu

November 13, 2025
Nijeriya Za Ta Buga Gasar Kofin Duniya Na Shekarar 2026 – Gusau

Nijeriya Za Ta Buga Gasar Kofin Duniya Na Shekarar 2026 – Gusau

November 13, 2025
‘Yan Wasan Ƙwallon Ƙafa 10 Da Za Su Iya Buga Gasar Cin Kofin Duniya Ta Ƙarshe A 2026

‘Yan Wasan Ƙwallon Ƙafa 10 Da Za Su Iya Buga Gasar Cin Kofin Duniya Ta Ƙarshe A 2026

November 13, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.