Gwamnatin jihar Yobe ta bayar da umarnin kwashe al’ummar Usur da Gasma da ambaliyar ruwa ta yi wa barazana a kananan hukumomin Bade da Karasuwa.
Mataimakin gwamnan jihar, Idi Gubana, ne ya bayar da wannan umarni a ranar Lahadin da ta gabata a Gashua lokacin da ya ziyarci yankunan da ambaliyar ruwa ta shafa a yankin.
- Ambaliyar Ruwa: Manoman Shinkafa Sun Karaya Da Samun Amfani Mai Yawa
- Ambaliyar Ruwa: Gwamnatin Yobe Ta Tallafa Wa Magidanta 457 A Karamar Hukumar Jakusko
Ya umurci hukumar bayar da agajin gaggawa ta jihar SEMA da ta kwashe mazauna Usur da Gasma zuwa sabon rukunin gidaje da aka gina a Jaji Maji.
Mataimakin gwamnan ya ce sun kai ziyarar ne domin jajantawa wadanda bala’in ya rutsa da su da kuma tantance irin barnar da aka yi domin samun tallafin da ya dace.
Gubana ya kuma umurci SEMA da ta samar da kayan agaji ga wadanda abin ya shafa domin rage musu radadi.
A nasa jawabin, Sarkin Bade, Abubakar Suleiman, ya gode wa mataimakin gwamnan bisa ziyarar ta’aziyyar da ya kai masa.
Ya kuma bukaci al’ummar yankin da su yi addu’ar Allah ya dawo mana da zaman lafiya a yankunan da lamarin ya shafa.
Mataimakin gwamnan ya samu rakiyar kakakin majalisar dokokin jihar Yobe Ahmad Mirwa da sakataren gwamnatin jihar Baba Wali da dai sauransu.