Gwamnan jihar Zamafara, Bello Mohammed Matawalle, ya hana Sarakunan jihar nadin sarauta har sai sun samu amincewar gwamnatin jihar.
A wata sanarwa da mai taimaka wa gwamnan kan kafofin yada, Zailani Bappa, ya fitar ”Daga yanzu an umarci duk Sarakuna, da Hakimai, da Dagatai da ke jihar da su nemi amincewar gwamnatin jihar kafin su nada kowa, a kowanne mukami na Sarautar gargajiya”.
- Kotu Ta Tabbatar Da Adeleke A Matsayin Dan Takarar PDP Na Asali
- Sojoji Sun Sake Ceto Daya Daga Cikin ‘Yan Matan Chibok A Borno
An ruwaito sanarwar ta ci gaba da cewa ”Umarnin ya zama wajibi ne domin kauce wa gurbata tsarin sarautar gargajiya, daga yanzu babu Sarki, ko Hakimi ko Dagacin da zai nada kowanne mukamin Sarauta, ba tare da samun amincewa da sahalewar gwamnatin jiha ba.
”Bin wannan doka ya zama wajibi, domin kuwa gwamnati ta tanadi kwakkwaran mataki ga duk wanda ya saba wa dokar”, in ji sanarwar.
Wannan na sanarwa na zuwa ne biyo bayan nadin sarautar Sarkin Fulani da masarautar ’Yandoto ta yi wa kasurgumin dan bindiga, Ado Aleiro.
Nadin sarautar ya bar baya da kura, lamarin da ta kai ga dakatar da sarkin na ‘Yantodo.