Gwamnatin jihar Zamfara ta kashe kimanin naira biliyan daya da Miliyan dari biyar (N1.5bn) domin gyara da inganta gidajen kwanan Dalibai da cibiyoyin ilimi guda biyu a jihar.
Makarantun da suka amfana sun hada da Makarantar Sakandaren Kimiyya da ke Gusau da Kwalejin Fasaha da Kimiyya ta Jihar Zamfara (ZACAS).
- Matsalar Tsaro: Ɗalibai Sun Ƙaurace Wa Ɗakunan Kwana A Lakwaja
- Monguno Ya Maye Gurbin Ndume A Matsayin Mai Tsawatarwar Masu Rinjaye A Majalisa
Da yake zantawa da manema labarai jim kadan bayan kammala duba ayyukan rukunin farko da aka kammala, Kwamishinan ilimi na jihar, Malam Wadatau Madawaki ya ce, kwangilar aikin ta biyo bayan ayyana dokar ta baci kan ilimi da Gwamna Dauda Lawal ya yi.
Kwamishinan ya bayyana gamsuwarsa da ingancin aikin da dan kwangilar ya yi a makarantun biyu da ya ziyarta.
Madawaki ya bayyana cewa, gwamnatin Gwamna Dauda Lawal na bada fifiko kan fannin ilimi wanda ya sanar da gyare-gyare da inganta ayyukan ilimi a jihar domin tabbatar da ingantaccen yanayin koyo da aiki ga dalibai da ma’aikata.
Ya yi nuni da cewa, a wannan sabon tsarin, gwamnatin jihar ta mayar da hankali ne kan ilimin kimiyya, fasaha da kasuwanci, domin cusa sana’o’i a cikin dalibai, musamman dalibai mata.
Kwamishinan Ilimi ya bukaci daliban kwalejin fasaha da kimiya ta jihar da su yi kyakkyawan amfani da sabbin kayayyakin aiki domin bunkasa ayyukansu na karatu.