Gwamnatin Zamfara ta tabbatar da mutuwar mutane 40 bayan wani hatsarin kwale-kwale a ƙaramar hukumar Gummi da ke jihar.
Rahotanni sun tabbatar da cewa jirgin kwale-kwalen ɗauke da mutane sama da 40 a ranar Lahadin da ta gabata ya kife a kogin Bakin Kasuwa na unguwar Uban Dawaki.
- Bayan Fafatawa, Ƴan Ƙauye Sun Hallaka Ƴan Bindiga 37 A Zamfara
- Rundunar Ƴansandan Jihar Zamfara Ta Tabbatar Da Kisan Jami’anta 4 Da Sojoji 3 Yau A Zamfara
Babban mataimaki na musamman ga gwamnan kan harkokin yaɗa labarai da yada labarai Sulaiman Idris, wanda ya tabbatar da faruwar lamarin, ya ce gwamnan ya bayyana lamarin a matsayin wani babban iftila’i.
Ya kuma ƙara da cewa gwamnan ya umarci kwamishinan agaji da ya kai kayan tallafi cikin gaggawa ga waɗanda abin ya shafa da iyalansu.
Idan dai za a iya tunawa, a baya-bayan nan ma dai wata ambaliyar ruwa ta lalata gidaje sama da 2000 da amfanin gona da dama da darajarsu ta kai miliyoyin Naira a ƙaramar hukumar.