Gwamnatin jihar Zamfara karkashin jagorancin gwamna Dauda Lawal za ta bai wa mata fifiko wajen walwalarsu saboda gudunmuwar da suka bada wajen samun nasara zabensa gwamna.
Kwamishinar Ma’aikatar mata da walwalarsu ce ta bayyyana haka lokacin da ta ke gabatar da jawabi a wajen wa’zin mako da ake gatarwa kowace Juma’a a ma’aikatar.
- Ambaliya: NEMA Ta Bada Tallafin Kayayyakin Agaji Ga Mutane 22,202 A Kebbi
- ‘Yan Bindiga Sun Hallaka Tsohowar Shugaban Kotun Gargajiya A Benue
A cewarta, gwamna Dauda Lawal ya dauki alwashin taimaka wa mata ta fanin lafiya da koya musu sana’oi don dogara da kansu kuwa wannan shi ne sakayyar da zai musu na ganin ya zamo gwamna a zaben da ya gabata.
Kuma wannan gwamnatin na da shirye-shirye musamman a kan mata don ganin sun amfana da wannan gwamnati da su kafata da hannunsu.
A kan haka ne ta yi kira ga matan jihar Zamfara da su dinga yi wa ‘ya’yansu addu’a don kada su biye wa miyagun halaye.
Kuma haka ita gwamnati na bukatar addu’a don ganin kudirinta ya cika na samun nasara dakile ayyukan ‘yan ta’adda.