Wasu daga cikin gwamnonin kasar nan, sun bukaci daukacin Musulmi da su yi amfani da lokutan Sallah wajen yin addu’oin samun zaman lafiya da magance kalubalen rashin tsaro da kuma samun ci gaba a kasa baki daya.
Daya daga cikin gwamnonin, gwamnan jihar Gombe Muhammadu Inuwa Yahaya a nasa sakon Sallah ga al’ummar jiharsa, ya nanata bukatar ci gaba da yin addo’oin samun zaman zaman lafiya a jihar da kuma kasa baki daya.
- Yadda Waliyin Amarya Ya Sace Sadaki A Kano
- Sakon Sallah: Ina Aiki Dare Da Rana Don Ceto Nijeriya -Tinubu
Sakon nasa na kunshe ne cikin sanarwar da Darakta Janar na yada labaransa Ismaila Uba Misilli ya fitar.
Gwamnan wanda kuma shi ne shugaban kungiyar gwamnonin Arewacin Nijeriya, ya bukaci ‘yan uwa Musulmi da su taimaka wa gajiyayyu da marasa karfi, kamar Annabawan Allah SWA, Ibrahim AS da Muhammad S.A.W Allah ya kara masa aminci suka kwadaitar da Musulmi suma su yi.
Shi kuwa, gwamnan jihar Neja Mohammed Umaru Bago, ya yi kira ne ga Musulmi da su rungumi dabi’ar kauna yin da’a kamar yadda kakanmu Annabi Ibrahim AS ya kwatar da Musulmi.
A nasa sakon, wanda sakatarensa na yada labarai Bologi Ibrahim ya fitar, gwamnan ya jaddada mahimmancin da babbar Sallar ta ke da shi, inda ya bukaci Musulmi da su yi amfani da damar don kara karfafa imaninsu da mika al’amuransu ga Allah SWA.
A nasa bangaren gwamnan jihar Filato, Barista Caleb Mutfwang ya yi kira ga Musulmi da su ci gaba da sadaukar da kawunansu wajen nuna kuna da son juna.
Mutfwang, a cikin sakon wanda Daraktansa na yada labarai Gyang Bere, ya fitar, ya bai wa ‘yan jihar tabbacin cewa, gwamnatinsa za ta ja kowa a jiki.
Shi ma gwamnan jihar Kwara AbdulRahman AbdulRazaq, ya taya Musulmi murnar bikin Sallah babba, inda ya ce Sallar na nuna yin imani ne da kuma mika wuya ga Allah SWA.
Shi kuwa gwamnan jihar Kogi Yahaya Bello, ya bukaci ‘yan jihar da su rungumi dabi’ar yin kyauta ga marasa karfi da kuma sadaukar da kai.
Bello, a sakon nasa ya shawarci Musulmi da su rungumi koyarwar Annabi Muhammad SAW ya koyar.
Shi ma sakararen gwamnatin tarayya Sanata George Akume a cikin sanarwar da ya fitar, ya taya Musulmi muranar Sallah, inda ya bukace su da su yi amfani da lokutan Sallar wajen nuna kauna da sadaukar da kai don samun zaman lafiya a Nijeriya.
Ita kuwa kungiyar dattawan Arewa (ACF) ta ya Musulmi murnar babbar Sallah.
ACF a cikin sanarwar da shugabanta, Architect Gabriel Aduku ya fitar ya bukaci Musulmi da su rungumi dabi’ar samun zaman lafiya da kuma yi addu’oi don Allah ya kawo dauki ga tattain arzikin Nijeriya.
Shi ma shugaban hukumar jin dadin alhazai ta kasa (NAHCON), Alhaji Zikrullah Kunle Hassan a sakonsa ya ta ya daukacin Musulmin duniya murnar bikin babbar Sallah.