• English
  • Business News
Wednesday, November 5, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Gwamnonin APC Sun Nemi Tinubu Ya Ƙirkiri ‘Yansandan Jihohi Don Yaƙar Matsalar Tsaro

by Sadiq
5 months ago
APC

Yayin da matsalolin tsaro ke ƙara ta’azzara a sassa daban-daban na Nijeriya, gwamnonin jam’iyyar APC mai mulki sun bayyana cikakken goyon bayansu ga Shugaba Bola Ahmed Tinubu. 

Haka kuma, sun buƙaci sauran gwamnonin jihohi da su ɗauki matakan kare al’ummominsu ta hanyar kafa ‘yansandan al’umma.

  • Lakurawa Sun Sanya Dokar Hana Sayar Da Shanu A Kebbi
  • An Kashe Wasu ‘Yan Bindiga 12, An Kwato Makamai A Katsina

Bayan wani taron sirri da ya ɗauki tsawon sa’o’i uku a Abuja, Shugaban Ƙungiyar gwamnonin APC kuma Gwamnan Jihar Imo, Hope Uzodimma, ya shaida wa manema labarai cewa suna tunanin kafa ‘yansandan jihohi bisa shawarar da Gwamna Hyacinth Alia na Jihar Benuwe ya bayar.

Gwamna Uzodimma ya ce za su ci gaba da mara wa Shugaba Tinubu baya domin ya cimma nasarar shawo kan matsalolin tsaro da ke addabar ƙasar.

A lokacin da Shugaba Tinubu ya kai ziyara Jihar Benuwe, Gwamna Alia ya yi kira da a kafa ‘yansandan jihohi a matsayin mafita ga matsalar tsaro.

LABARAI MASU NASABA

Majalisar Kano Na Tattauna Batun Fara Amfani Da Harshen Hausa A Wurin Koyarwa A Makarantu 

ECOWAS Ta Ƙaryata Iƙirarin Trump Kan Kisan Kiristoci A Nijeriya

Ya ce duk da cewa akwai damuwa kan yadda za a aiwatar da hakan, Gwamnatin Tarayya na da damar tsara ƙa’idoji da dokoki na musamman ga kowace jiha don hana amfani da ‘yansandan wajen cin zarafi.

A halin yanzu, gwamnonin jihohi daga faɗin Nijeriya na gudanar da wani taron gaggawa a Babban Birnin Tarayya, wanda ke gudana a sakatariyar Ƙungiyar Gwamnonin Nijeriya (NGF).

Taron ya samu halartar gwamnonin jihohi da mataimakansu daga dukkanin jihohi 36 na ƙasar.

Koda yake ba a bayyana cikakken ajandar taron ba, kasancewar mai bai wa shugaban ƙasa shawara kan harkokin tsaro, Nuhu Ribadu, da Ministan Tsaro, Mohammed Badaru, na cikin mahalarta taron, ya nuna cewa batutuwan tsaro ne ke kan gaba a tattaunawar.

Taron na gaggawa na zuwa ne a daidai lokacin da tsaro ke taɓarɓarewa a sassa da dama na ƙasar, lamarin da ke ƙara haifar da kira daga al’umma da shugabanni domin ɗaukar matakin gaggawa da haɗin gwiwa tsakanin jihohi da Gwamnatin Tarayya.

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

Majalisar Kano Na Shirin Zartar Da Dokar Gwajin Kwayoyin Jini, Kanjamau Da Cutar Hanta Kafin Aure
Manyan Labarai

Majalisar Kano Na Tattauna Batun Fara Amfani Da Harshen Hausa A Wurin Koyarwa A Makarantu 

November 5, 2025
An Nemi Kasashen ECOWAS Su Samar Da Kariya Ga Yankunan Hakar Ma’adanai
Manyan Labarai

ECOWAS Ta Ƙaryata Iƙirarin Trump Kan Kisan Kiristoci A Nijeriya

November 5, 2025
Tsohon Shugaban Ma’aikatan Fadar Shugaban Ƙasa, Ya Rasu Yana Da Shekaru 86
Da ɗumi-ɗuminsa

Tsohon Shugaban Ma’aikatan Fadar Shugaban Ƙasa, Ya Rasu Yana Da Shekaru 86

November 5, 2025
Next Post
Masarautar Gaya Ta Ƙwace Sarautar Wazirin Gaya Da Ta Bai Wa Tsohon Sakataren Gwamnatin Kano

Masarautar Gaya Ta Ƙwace Sarautar Wazirin Gaya Da Ta Bai Wa Tsohon Sakataren Gwamnatin Kano

LABARAI MASU NASABA

Dantsoho Ya Nemi Hadin Kan Kasashen Afrika Wajen Bunkasa Tashoshin Jiragen Ruwa

Dantsoho Ya Nemi Hadin Kan Kasashen Afrika Wajen Bunkasa Tashoshin Jiragen Ruwa

November 5, 2025
Nazarin Cgtn: Kasashe Masu Tasowa Sun Yi Kira Da A Inganta Tsarin Tafiyar Da Harkokin Duniya

Nazarin Cgtn: Kasashe Masu Tasowa Sun Yi Kira Da A Inganta Tsarin Tafiyar Da Harkokin Duniya

November 5, 2025
Gwamna Yusuf

Malam Triump: Ƙungiyoyin Ɗariƙun Sufaye Sun Maka Gwamnan Kano A Kotu

November 5, 2025
An Rufe Canton Fair Na 138 A Guangzhou

An Rufe Canton Fair Na 138 A Guangzhou

November 5, 2025
Sabbin Ministoci

Majalisa Ta Nuna Damuwa Kan Rahoton Yiwuwar Asarar Dala Biliyan 300 A Badaƙalar Ɗanyen Mai

November 5, 2025
Firaministan Kasar Sin Ya Gabatar Da Jawabi A Bikin Bude CIIE 

Firaministan Kasar Sin Ya Gabatar Da Jawabi A Bikin Bude CIIE 

November 5, 2025
Majalisar Kano Na Shirin Zartar Da Dokar Gwajin Kwayoyin Jini, Kanjamau Da Cutar Hanta Kafin Aure

Majalisar Kano Na Tattauna Batun Fara Amfani Da Harshen Hausa A Wurin Koyarwa A Makarantu 

November 5, 2025
Sin Za Ta Gyara Matakan Haraji Kan Kayayyakin Da Ake Shigowa Da Su Daga Amurka

Sin Za Ta Gyara Matakan Haraji Kan Kayayyakin Da Ake Shigowa Da Su Daga Amurka

November 5, 2025
Kundin Tsarin Mulkin Nijeriya Bai Yadda Da Tauye Haƙƙin Addini Ba – Minista

Kundin Tsarin Mulkin Nijeriya Bai Yadda Da Tauye Haƙƙin Addini Ba – Minista

November 5, 2025
…ACF Ta Nesanta Kanta Da Goyon Bayan Akpabio

Majalisar Dattawa Ta Amince da Naira Tiriliyan 1.1 Don Biyan Bashin ‘Yan Kwangila – Akpabio

November 5, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.