Shugaban Gwamnonin Arewa Maso Gabas, Gwamna Babagana Umara Zulum, ya shaida cewar, shirye-shirye sun yi nisa na samar da kamfanin zirga-zirgan Jirgin sama mai suna ‘North-East Airline’.
Zulum wadda ya shaida hakan a lokacin da ke bude taron ganawar kungiyar Gwamnonin Arewa Maso Gabas karo na bakwai da ke gudana yanzu haka a jihar Gombe.
- Ambaliyar Ruwa: Gwamnatin Yobe ta tallafa wa magidanta 457 a karamar hukumar Jakusko
- Farfadowar Tattalin Arzikin Kasar Sin Ya Zarce Yadda Ake Tsammani
Ya kara da cewa, taron nasu zai fi maida hankali kan lamuran da suka shafi tsaro, magance matsalolin Boko Haram, garkuwa da mutane, dumamar yanayi da kuma kalubalen ambaliyar ruwa da ake samu hadi da sauran muhimman batutuwa ciki har da batun samar wa matasa da ayyukan yi.
Gwamna Babagana Zulum ya kara da cewa kungiyar gwamonin Arewa Maso Gabas (NEGF) ta samu nasarar kulla alakar yin aiki tare da Gwamnatin tarayya ta hannun hukumar bunkasa shiyyar Arewa Maso Gabas (North-East Development Commission), bankin duniya, da wasu abokan jere domin samar da damarmakin ayyukan yi ga matasa da suke yankin domin yaki da matsalar fatara da talauci.
Da ya ke jawabi maraba da baki, mai masaukin baki, Gwamna Muhammadu Inuwa Yahaya na jihar Gombe, ya yi fatan cewa zaman masu zai kai ga cimma muhimman batutuwa da za su taimaka wa shiyyar da al’ummarsu.
Ya marabci bakin da suka zo daga sassan jihohin shiyyar tare da basu tabbacin jin dadin rayuwa a jihar.