Gwamnoni 19 na Arewacin Nijeriya a karkashin kungiyar gwamnonin arewa sun bayyana aniyarsu ta tabbatar da dunkulewar yankin domin cin cikakkiyar gajiyar albarkatun kasa da na al’umma da Allah ya shinfida a yankin.
A kan haka suka dawo da taken shugabanin yankin na farko suke yi ma yankin na “Kasa Daya Makoma Daya”. Hadin kai da aiki tare da zai taimaka wajen fuskantar dukkan kalubalen da yankin ke fuskanta. Gwamnonin sun kuma nemi a hada kai a fuskanci matsalar tsaron da ta addabi yankin.
Kiran Minista Ga VON: Ku Yaɗa Kyawawan Labarun Nijeriya Ga Duniya
Gwamnati Ta Shirya Fatattakar ‘Yan Bindiga A Duk Inda Suke – Ministan Tsaro
Shugaban kungiyar gwamnonin arewa kuma Gamnan Jihar Gombe, Alhaji Muhammadu Inuwa Yahaya ya bayyana haka a taron da kungiyar ta gudanar a Kaduna a makon jiya.
“Tabbatar da hadin kai shi ne mabudin ci gaban yankin Arewacin Nijeriya, za mu dawo da akidar Arewa Daya Makoma Daya kamar yadda iyayenmu suka shimfida don samar da cikakkiyar hadin kai da soyayyar juna ba tare nuna banbancin siyasa, kabilanci ko addini ba” in ji shi.
Shugaban kungiyar gwamnonin ya kuma yi kira ga ‘yan siyasa, sarakunan gargajiya, malaman addini da dukkan masu ruwa da tsaki su rungumi juna da nufin samar da ci gaban da ake bukata a sassa daban-daban na tattalin arzikin yankin.
Ya kuma ce, “A mastayimu na gwamnaonin yankin arewa 19 muna yaba wa yukurin gwamnatin tarayya na kokarin kawo karshen matsalar tsaron da ta addabi yankin musamman ayyukan masu garkuwa da mutane, da ayyukan ‘yan bindiga a sassan yankin”.
“Tsaro da ci gaban al’umma abu ne da suke tafiya tare in har babu tsaro to lalai babu ci gaba don masu zuba jari ba za su shigo ba har a samu ayyukan yi ga matasanmu.”
Ya kuma ce, ba za a samu damar gudanar da ayyukan hanyoyi da gadoji ba da sauran ayyukan raya kasa ba har sai an samu tsaro da zaman lafiya, da wannan ne manoman mu za su saki jiki su noma abincin da za a ciyar da Nijeriya.
A nasa jawabin, Gwamnan Jihar Kaduna, Uba Sani ya lura da cewa, matsalar tsaro ta dade tana ci wa yankin arewa tuwo a kwarya, a kan haka ya nemi shugabanin yankin su hada kai tare da fito da dabaru iri daya wajen tunkarar matsalar tsaro bai-daya a yankin.