Kungiyar Gwamnonin Arewa 19 Sun Tallafawa wadanda harin bam na Tudun Biri a Karamar Hukumar Igabi da ke Jihar Kaduna da kudi Naira miliyan 180 a matsayin gudummawa domin rage musu radadin asarar da suka yi.
Shugaban kungiyar gwamnonin Muhammadu Inuwa Yahaya, shi ne ya sanar da hakan a jawabin bayan taron kungiyar tayi a Kaduna yau Juma’a a fadar gwamnatin Jihar Kaduna.
- Kawancen Yakar APC: Jam’iyyun Adawa Sun Shiga Dimuwa
- Da Gangan Aka Cire Aikin Mambilla A Kasafin 2024 – Ministan Lantarki
Mohammad Inuwa Yahaya, wanda shi ne gwamnan Jihar Gombe, ya jajantawa gwamnatin Jihar Kaduna da daukacin al’ummar Tudun Biri bisa iftila’in da ya same su a kwanan baya.
Kazalika, kungiyar ta bukaci da a gudanar da bincike mai tsauri domin kaucewa farun irin wanan harin nan gaba, tare da hukunta wadanda suke da hannu wajen kai harin.
Kungiyar ta kuma yaba da qoqarin gwamnatin tarayya Dana Jihar Kaduna bisa daukar matakan gaggauwa wajen tallafawa wadanda suka jikkata da yunkurin kula da al’ummar Tudun Biri.
Gwamnonin Sun kuma koka dangane da yadda matsalar rashin tsaro yake ta’azzara a yankin Arewacin kasar nan, suna mai daukar alwashin kawo karshen matsalar sace mutane da na ‘yan bindiga a yankin.
Akan hakan kungiyar ta yi alkawarin tallafawa rayuwar matasa ta hanyar samar musu da aikin wanda hakan Yana daga cikin matakan da suke dauka na yakar talauci da matsalar rashin tsaro a fadin yankin baki daya.