Ƙungiyar Gwamnonin Jihohin Arewa (NSGF) ta bayyana alhininta game da mummunar fashewar tankar mai da ta yi sanadin mutuwar mutane da dama a garin Essa da ke ƙaramar Hukumar Katcha ta Jihar Neja.
Da ya ke tsokaci kan wannan mummunan lamari, Shugaban Ƙungiyar ta Gwamnonin Arewa kuma Gwamnan Jihar Gombe, Muhammadu Inuwa Yahaya, ya miƙa saƙon ta’aziyyarsa ga gwamnati da al’ummar Jihar Neja, musamman ga iyalan waɗanda suka rasu da kuma Gwamna Mohammed Umar Bago, bisa mummunan hatsari da ya yi sanadin mutuwar mutane da dama tare da jikkata wasu da dama.
- Ba A Yi Wa Kiristoci Kisan Gilla A Arewacin Nijeriya – Sarkin Musulmi
- Shugabannin jam’iyyar PDP Na Arewa Sun Amince Da Turaki A Matsayin Ɗan Takarar Shugabancin Jam’iyyar Na Ƙasa
A sanarwar da mai magana da yawun gwamnan, Ismaila Uba Misilli ya fitar, Gwamnan ya ce “Wannan bala’i yana da matuƙar ciwo da tada hankali, tunani da addu’o’inmu suna tare da iyalan da wannan ibtila’in ya shafa, da kuma gwamnati da al’ummar Jihar Neja a wannan lokaci na baƙin ciki”.
Ƙungiyar ta yi amfani da wannan lokacin don yin ƙira da a ƙara wayar da kan jama’a game da matakan kariya da kuma tsaurara matakan tsaro kan yadda ake safara da adana fetur da sauran dangoginsa. Haka kuma ta gargaɗi jama’a kan illolin dake tattare da ribibin zuwa ɗiban fetur da yin wasu munanan ɗabi’u a lokacin da irin wannan lamari ya faru.
Gwamna Inuwa Yahaya ya ƙara da cewa, “Wannan abin takaici yana nuna matuƙar buƙatar inganta matakan kariya da wayar da kan jama’a kan illolin dake tattare da safarar man fetur, dole ne gwamnatoci, hukumomi da jama’a su haɗa kai don hana afkuwar irin wannan lamari.”
Sai dai ya yabawa masu ba da agajin gaggawa, da jami’an tsaro da kuma ‘yan sa-kai da suka yi aiki tuƙuru wajen ceto waɗanda lamarin ya rutsa da su, tare da ba su agaji, yana mai cewa ɗaukin gaggawan da suka kai ya taimaka wajen rage munin ibtila’in.
A yayin da take addu’ar Allah ya jiƙan waɗanda suka rasu ya kuma bai wa waɗanda suka jikkata lafiya cikin gaggawa, ƙungiyar Gwamnonin Arewan ta bada tabbacin cewa za ta ci gaba da haɗa hannu da hukumomin tarayya dana jihohin da abin ya shafa don ƙarfafa tsarin rigakafi da ɗaukar matakan kare rayuka da dukiyoyin al’umma.














