A yayin da jihohin Arewacin kasar nan suke ci gaba da fuskantar matsalar rashin wutar lantarki, wadda ta shafi ma’aikatun gwamnati da masana’antu da kuma harkokin kasuwancin al’ummar yankin arewa, da aka kwashe kwanaki babu hasken wutar lantarki a yankin, wasu na ganin shiryayyen lamari ne na yi wa tattalin arzikin yankin zagon kasa.
Kungiyar dattawan arewa (NEF) ta bayyana cewa matsalar rashin wutar lantarki a arewa shiryayyen lamari ne, inda suka ce an yi haka ne domin yi wa tattalin arzikin arewa zagon kasa.
- Ba Zan Goyi Bayan Ƙudirin Ƙarin Haraji Ga Talakawa Ba – Sanata Ndume
- Horor Da Kasar Sin Take Tallafawa Ya Inganta Yaki Da Nakiyoyin Da Aka Binne A Somaliya
A zantawarsa da wakilinmu, mai magana da yawun kungiyar dattawan Arewa, Abdul-Azeez Suleiman, ya ce, “Ga dukkan mai hankali da kuma kishin Arewa ya san zagon kasa ne da nufin gurgunta yankin. Idan aka yi la’akari da abubuwan da ke faruwa kafin rashin wutar, za a ga cewa rashin zaman lafiya ya hana noma, ya hana kiwo, ya hana karatu a Arewa. Yanzu ga wannan bakin duhu da aka jefa yankin a ciki.
“Masana sun tabbatar da cewa idan ana nufin gurgunta kasa ko yanki ko al’umma, matakin farko shi ne jefa ta cikin duhu. A yanzu a Arewa ba masana’antar da ke motsawa, ko nikan tuwo da garin kunu ya zama tashin hankali. Kun ga kenan duk matakai na gurgunta tattalin arziki da walwala da zaman lafiya duk sun bayyana. Sai dai fa Arewa ba ta da ikon zargin wani yanki game da wannan lamari.
Ya ci gaba da cewa, tun bayan mulkin su Sardauna Ahmadu Bello aka sami wadanda ba su damu da al’umma ba, sai kawunansu da iyalansu, suke ta sace dukiyoyi suna mayar da Arewa baya. Ya ce shugabannin Arewa su suka kashe duk ababen more rayuwa da Sardauna ya samar.
Sai dai a nata bangaren, kungiyar gwamnonin Arewa ta nemi gwamnatin tarayya ta yi gaggawar shawo kan matsalar wutar lantarki da ake fama da ita a mafi yawan yankin.
Kungiyar ta yi kiran ne yayin taron da ta gudanar a fadar gwamnatin Jihar Kaduna karkashin jagorancin Gwamnan Gombe, Muhammadu Inuwa Yahaya.
Gwamnonin tare da sarakunan gargajiya na shiyyar Arewacin kasar nan sun tattauna matsalolin da suka dabaibaye yankin. Sama da kwana takwas kenan da jefa yankunan Arewa maso yamma, da Arewa maso gabas, da wani bangare na Arewa ta tsakiyar cikin duhu sakamakon lalacewar babban tashar samar da wutar lantarki ta kasa.
Gwamna Inuwa ya kara da cewa, “Kungiyar na kira ga gwamnatin tarayya da hukumomin da suka dace da su gaggauta shawo kan matsalar lantarki da mafi yawan jihohin arewaci ke ciki.
“Wannan lamari ba wai yana nuna girman hadarin rashin ababen more rayuwa ba ne kawai, yana kuma fito da bukatun gina wasu hanyoyin fadada samun wutar lantarki.”
A wata sanarwar da hukumar kula da wutar lantarki na Nijeriya (TCN) ta fitar, ta ce matsalar rashin wuta da ke addabar yankin Arewa za ta ci gaba saboda kalubalen tsaro da ke hana gyaran wasu muhimman layukan wutar.
Ya zuwa yanzu a Jihar Kaduna matsalar rashin wutar lantarki tana ci gaba da jefa al’umma cikin mawuyacin hali a yayin da harkokin kasuwanci suka yi tsaye cak.
Sai dai kuma matsalar ta kara yawaitar ‘yan ta’adda musamman masu kwacen wayar hannu a wuraren da ake yin cajin wayoyi.
Masu shagunan cajin waya sun shaida wa wakilinmu cewa a kullum suna zama cikin fargabar matasa masu zuwa da makamai suna kwace wayoyin mutane da suka kawo caji.