Shugaban Kungiyar Gwamnonin Jihohin Arewa kuma gwamnan jihar Gombe, Muhammadu Inuwa Yahaya ya mika ta’aziyyarsa ga fitaccen dan kasuwar nan, Alhaji Dahiru Mangal bisa rasuwar matarsa Hajiya Aishatu Mangal.
Aishatu Mangal ta rasu a ranar Asabar din da ta gabata bayan gajeriyar rashin lafiya.
- Sarakuna Sun Yi Maraba Da Shirin Ba Su Dama Da Majalisar Wakilai Ta Yi
- Dajarar Naira Ta Sake Faduwa Zuwa 803 Akan Kowace Dalar Amurka
A sakonsa na ta’aziyya dauke da sanya hannun hadiminsa, Ismaila Uba Misilli, gwamnan ya bayyana rasuwar Hajiya A’ishatu a matsayin mai matukar zafi, kuma babban rashi, ba ga iyalan Mangal kadai ba har ma da Arewa da ma kasa baki daya.
“Mun yi matukar alhini da jin labarin rasuwar matarka, rasa mata ba abu ne mai sauki ba, amma nasan cewa kai mutum ne mai karfin hali da juriya, babu shakka muna tare da kai da iyalinka cikin wannan jimami tare da taya ku addu’o’i a wannan mawuyacin lokaci.
“Za a yi ta tunawa da marigayiya Hajiya A’ishatu a matsayin mace mai kirki, mai kyakkywar zuciya, kuma uwa mai karamci wadda a rayuwarta ta amfani mutane da dama. Abubuwan da ta yi za su ci gaba da wanzuwa tsawon shekaru masu zuwa”.
Gwamnan ya mika ta’aziyyar gwamnati da al’ummar Jihar Gombe ga Gwamnatin Jihar Katsina da dukkan wadanda marigayiyar ta bari game da wannan babban rashi, inda ya yi addu’ar Allah ya jikanta yasa Aljannar Firdausi ce makomar ta.