Terminal, ya kasancewa kamfanin mai na cikin gida ɗaya tilo da ya bunƙasa tashar fitar mai, Green Energy International Limited (GEIL) shi ne gwarzon kamfanin smar da abubuwan gid ana mai da gas na shekara ta 2025.
Kamfanin Green Energy International Limited (GEIL) ya cimma babbar nasara a ɓangaren man fetur da gas na Nijeriya tare da ƙaddamar da tashar fitar da mai na Otakikpo Onshore. Wannan aikin ya laƙume dala miliyan 400, ana yabonsa a matsayin tashar fitar da mai ta cikin gida gaba ɗaya ta farko da aka gina a Nijeriya cikin sama da shekaru 50.
- Gwarzon Kamfanin Samar Da Kaya Na Shekarar 2025, Kamfanin Nestlé Pure Life
- Gwarzon Kamfanin Fasahar Kuɗaɗe Na Shekarar 2025, Opay Nigeria
Saboda tashar fitar man fetur ta Otakikpo Onshore, kamfanin Green Energy International ya kafa sabon matsayi a ci gaban man fetur da gas na cikin gida, wanda ya sa ya cancanci yabo a matsayin jagora wajen amfani da kayan gida da kuma bunƙasa makomar makamashin Nijeriya.
Jagorancin Farfesa Anthony Adegbulugbe, GEIL yana nuna shugabanci mai hangen nesa da ƙarfi na fasaha, yana kawo manyan ayyukan makamashi na duniya zuwa zahiri a cikin ƙasa a shekaru biyu. Tashar Otakikpo da ke Jihar Ribas, yana da ƙarfin ajiye ganga mai 750,000 tare da tsare-tsaren faɗaɗawa zuwa ganga miliyan uku a nan gaba. Yana da ƙarfin fitar da ganga 360,000 a kowace rana don ɗora wa tankokin, yana samar da muhimmin na mai wanda aka ƙera don ɗaukar ganga 250,000 a kowace rana.
Wannan kamfani ya kawo ci gaba wajen buƙata ta dabarun tattalin arziki ta hanyar buɗe sama da filayen mai 40 da ke maƙale a kusa da ita, inda ake kiyasin ajiyar mai fiye da ganga biliyan uku a ciki. Tashar Otakikpo tana ƙara inganta harkokin jigilar mai a Nijeriya, tana rage dogaro da tashoshin mai na teku, sannan tana goyon bayan ƙoƙarin gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu na farfado da filayen mai na Ogoni da Opobo, waɗanda ba a bunkasa su ba tsawon sama da shekaru 30.
Aikin, wanda ke wakiltar tashar fitar da ɗanyen fetur ta farko da kamfanin Afirka mai zaman kansa ya bunƙasa a ƙasar, yana nuna babban jarin da ya wuce dala miliyan 400 a matakin farko, inda ake sa ran kuɗin zai ci gaba da bunƙasa har ya haura dala biliyan 1.3.
GEIL, ƙarƙashin jagorancin Farfesa Anthony Olusegun Adegbulugbe, wani sanannen malami kuma ƙwararren masani a fannin tsare-tsaren makamashi, yana da ƙwarewa mai sosai a tsawon shekaru masu yawa. Yana aiki a matsayin shugaban jami’ar Joseph Ayo Babalola da ke Jihar Osun, ya kuma kasance babban mai ba da shawara kan makamashi ga tsohon shugaba ƙasa, Olusegun Obasanjo. Haka kuma ya kasance shugaban shirin “National Gas to Power” na Nijeriya kuma ya ba da gudummawa ga rahotannin majalisar harkokin kasashen duniya kan sauyin yanayi (IPCC), waɗanda suka sami lambar yabo ta Nobel ta zaman lafiya a shekara ta 2007. Adegbulugbe an san shi da tsara manufofin makamashi na Nijeriya da inganta hanyoyin makamashi masu kula da muhalli.
Farfesa Adegbulugbe ya kasancewa yana riƙa muƙami biyu na shugaban kwamitin gudanarwa da kuma shugaban Kamfanin Green Energy International, yana kawo haɗin kai na ilimi da jagorancin masana’antu na ainihi. Dogon tarihinsa na ba da gudummawa ga manufofin makamashi da kuma fafutuka don magance matsalolin makamashi na cikin gida ya bayyana a cikin ayyukan kamfanin GEIL, wanda ya haɗa da tashar wutar lantarki mai ƙarfin 20MW (za a iya faɗaɗa zuwa 40MW) da tashar iskar gas mai nauyin 12 miliyan ta Otakikpo Midstream Ltd (FOML), waɗanda ke ƙara inganta harkokin makamashi a Nijeriya.
An yaba wa ƙwararrun ma’aikatan kamfanin GEIL na gida da haɗin gwiwarsu da hukumomin da ke kula da doka saboda saurin aiwatarwa da nasara na wannan babban aikin ingantaccen tsarin ƙasa da ƙasa.
Bisa ga wannan nasara, kamfanin Green Energy International Limited ya kasance a matsayin jagora a fannin makamashi na Nijeriya, yana nuna ƙarfin ƙasa wajen bayar da kayan aikin fitar mai na gida masu tasiri sosai. Tashar Otakikpo ta tsaya a matsayin shaida ga ƙudirin Nijeriya na faɗaɗa kayan aikin makamashi, zurfafa kuɗaɗe shiga da kuma ƙarfafa tsaron makamashi na ƙasa, wanda ya sanya GEIL ya dace da samun yabo a matsayin gwarzon kamfann bunƙasa abubuwan gida a masana’antar mai da gas.













