Adaidai lokacin da ake da ake fama da matsalar taɓarɓarewar tattalin arziƙi da rashin jin daɗin jama’a da kuma wahalhalun da suka biyo bayan sauye-sauyen da aka samu, Sanata Oluremi Tinubu ta kasance mai matuƙar tausayi da jin ƙai a tsarin harkokin mulki. A matsayinta na Uwargidan Shugaban Nijeriya, ta nuna cewa; idan aka aiwatar da mulki ta hanyar kyakkyawan jagoranci da tausayi da kuma tarbiyya, zai iya taimakawa wajen samun walwala ga dukkannin al’ummar ƙasa.
Shirin nan na ‘Renewed Hope Initiatiɓe’, ya mayar da Ofishin Uwargidan Shugaban Ƙasar ya zama abin koyi wajen yin hidima ga ‘yan ƙasa mai matuƙar ma’ana. Aikin da take gudanarwar, ya ƙunshi taimaka wa waɗanda mazajensu suka mutu, suka bar su da ƙananan yara, ɗalibai, tsofaffi da kuma nakasassu a dukkanin faɗin Nijeriya.
Yadda Ake Gina Ɗan’adam
Shirin ‘Renewed Hope Initiatiɓe’, ba aikin agaji ba ne; cibiyar sadar da jin kai ce ta ƙasa da aka ƙirƙira ta hanyar wani kyakkyawan tsari. A 2025 kaɗai, ayyukanta sun haura na Naira biliyan 25, wanda za a iya cewa; shi ne mafi girman aiki ko tallafin da uwargidan shugaban Nijeriya ta taɓa bayarwa.
Tun daga Jihar Kaduna zuwa Nasarawa, Benuwe zuwa Neja da kuma ma wasu jihohin, tawagar uwargidan shugaban ƙasar ta tallafa musu ta ɓangarori daban-daban. Ko dai, bayar da ƙaramin jari ga ‘yan kasuwa, kayan agaji ga waɗanda ambaliyar ruwa ta shafa ko kuma bayar da tallafin ilimi ga ɗalibai, wannan tsari nata ana aiwatar da shi cikin sauƙi kuma a tsare tare da bibiya.
- Uwargidan Tinubu Ta Ƙaddamar Da Ɗakin Karatu Na E-learning A Zamfara
- Sanatan Bauchi Ta Arewa Ya Fice Daga Jam’iyyar PDP
Har ila yau, shirin nan nata Mata A Aikin Noma, ya bai wa matan karkara sama da 20,000 tallafi da horarwa da ƙara samun kuɗin shiga ga iyalai da kuma wadatar da al’umma. Kazalika, shirin Tallafin Ilimi, ya samar wa fiye da ɗalibai 3,000, guraben karatu, kwamfiyutoci da kuma jagoranci na gari. Ga tsofaffi kuma, Asusun Tallafa wa Tsofaffi ya bai wa tsofaffi 5,000 alawus-alawus da kula da lafiyarsu tare kuma da maido da martabar musamman waɗanda aka yi watsi da su, aka kuma manta da su.
Lokacin da iftila’i ya afku a Jihohin Filato da Benuwe a tsakiyar 2025, ba saƙo ta aike da shi; cikin gaggawa ta garzaya domin jajanta musu. Ta ziyarci waɗanda abin ya shafa, ta jajanta wa waɗanda suka rasa matsugunansu, sannan ta bayar da gudummawar Naira biliyan ɗaya ga kowace jihohin guda biyu. Daga baya a watan Agusta, ta ba da irin wannan agaji da ya kai kimanin Naira biliyan ɗaya ga al’ummomin da ambaliyar ruwa ta shafa a Jihar Neja tare da buhunhunan shinkafa da kayan sawa 2,000.
A watan Satumba, ta mayar da bikin cikarta shekaru 65 zuwa hidimar ƙasa, inda ta tara kuɗi kimanin Naira biliyan 20.4, domin kammala ginin ɗakin karatu na ƙasa da aka daɗe ba a yi ba tare da yin watsi da shi a Abuja. Sannan, ta ƙi karɓar wasu kyaututtuka da aka ba ta, wanda hakan ke nuna kyakkyawan shugabanci na-gari.
Tausaya Wa Nakasassu
Tausayinta ga nakasassu ya bayyana a fili cikin shirin nan ‘Renewed Hope Initiatiɓe’, a ɓangaren nan na koyar da sana’a’i, wanda ya horar da aƙalla mutum 1,200 ilimin kwamfuta, samar da ‘yan kasuwa tare da horar da wasu. Ta kuma ba da tallafin kiwon lafiya da wayar da kan jama’a tare da tantance ‘yan Nijeriya sama da 100,000 masu fama da cututtukan hawan jini, ciwon siga da kuma matsalar ido, domin tabbatar da ko suna ɗauke da cututtukan tare da ɗaukar matakan gaggawa.
Ta hanyar dagewa wajen ganin shirin ya tafi yadda ya kamata, Sanata Tinubu ta gabatar da kyakkyawan tsari, domin aiwatar da ayyukan jin ƙai. Dagewarta kan nuna gaskiya, ya sa shirin RHI ya samu karramawa daga ƙungiyoyin farar hula da sauran abokan ci gaban ƙasa da ƙasa.
Sabunta Harkokin Ilimi
Tsohuwar malamar makaranta, Sanata Tinubu na kallon ajujuwa a matsayin wurin da aka samar da sabbin sauye-sauye. Shirin da ta samar na matasa masu ilimi, wanda aka ƙaddamar a shekarar 2024, aka kuma sake faɗaɗa shi a 2025, na tallafa wa ɗalibai masu hazaƙa, waɗanda iyayensu ke da ƙaramin ƙarfi (Talakawa), wanda ya dace da su tare da ba su shawarwari, musamman ta fuskar harkar ilimin kimiyya da fasaha. Fiye da ɗalibai 1,200 a halin yanzu sun samu damar shiga shirin, wanda ke nuni da cewa; sama da kashi 95 cikin 100 na waɗanda suka rabauta, ba su taɓa mantawa da wannan abin alhairi da aka yi musa ba.
Tasirin Abin Da Za A Iya Ƙirgawa Da Kuma Wanda Ke Shafar Ruwa Kai Tsaye
A duk fadin Najeriya, za a iya ƙirga ayyukanta, ba kawai a ƙididdiga ba, a cikin labarai.
Mata manoma 20,000 a halin yanzu, suna samun kuɗin shiga akai-akai, saboda tallafin noma da horo na RHI. Dubban ɗalibai, sun faɗa kasadar ficewa daga makarantusu, amma yanzu ƙarƙashin wannan shiri nata, sun koma azuzuwansu sakamakon bayar da tallafin karatun da ta yi.
Haka zalika, sama da ‘yan Nijeriya 100,000 ne aka yi wa gwajin kamuwa da cututtuka masu tsanani daban-daban, sannan da dama daga cikinsu sun samu tallafin ceton rai. Yanzu haka, tsofaffi dubu biyar ne ke cin gajiyar alawus-alawus na yau da kullun da kuma zuwa duba lafyarsu, yayin da nakasassu kuma aka ba su kayan aiki, domin fara sana’o’insu, wasu kuma da kansu sun zama masu horar da su.
A kowane irin hali, alƙalumman na ba da labari iri guda: a ƙarƙashin Sanata Tinubu, tausayi ya zama shi ne abin aunawa, sannan kuma abubuwan da ake sa rai da su, sun tabbata.
Imani, Iyali da kuma Amfanin Shugabanci
Kasancewarta mai tsananin tausayi da gaskiya, jagora tagari, mai kuma son yin aiki ta hanyar yin haɗin gwiwa, Sanata Tinubu na ɗaya daga cikin waɗanda ke jagorantar al’ummar da samar da haɗin kai tare da tausayinsu. Ta auri Shugaba Bola Ahmed Tinubu, sannan ta daidaita buƙatun shugabancin ƙasa da iyali, imani da kuma tawali’u.
Nutsuwa da halinta da kuma ɗabi’un aikinta, sun haifar da sha’awa; har ma daga masu suka, suna sake fasalin ofishin Uwargidan Shugabancin a matsayin ɗaya daga cikin kulawa, maimakon alama. Ta nuna cewa, mulki a cikin lumana, ka iya haifar da sakamako mai kyau tare da kuma tausayi.














