Domin samun fata mai laushi, sumul, da haske kamar kwai.
1. Maganin kurajen da Laushin fuska
Abubuwan hadawa:
Bawon lemon tsami, bawon kwai, ruwa
Yadda ake hadawa:
Ki shanya bawon lemon tsami da na kwai su bushe, ki daka su sosai har su yi laushi. Ki kwaba da ruwa kadan, sannan ki shafa a fuskarki kafin wanka.
2. Gyaran Fuska da tumatir
Abubuwan hadawa:
Tumatir, madara
Yadda ake amfani:
Ki markada tumatir, ki zuba madara, ki kwaba. Ki shafa a fuska, ki bar shi na minti 30, sannan ki wanke da ruwan dumi.
3. Gyaran fuska da garin alkama
Abubuwan hadawa:
Garin alkama, Zuma, madara
Yadda ake amfani:
Ki hada su wuri guda, ki shafa a fuska kafin ki shiga wanka. Zai sa fata ta yi laushi sosai.
4. Laushin fata da lemo tsami
Abubuwan hadawa:
Lemon tsami, Zuma
Yadda ake amfani:
Kafin kwanciya barci, ki hada lemon da zuma ki shafa. Da safe, ki wanke da ruwan dumi, zai haskaka fata kuma ya hana kuraje.
5. Man shafawa domin Laushin jiki
Abubuwan hadawa:
Man kwakwa, man kade, man angurya, man zaitun, Almond oil, baby oil, madarar turare, cocoa butter
Yadda ake amfani:
A hada dukkan mayukan, a zuba a kwalba. Ki rika shafawa bayan wanka. Jikinki zai yi laushi, santsi da kamshi.
6. Sabulun wanka na musamman
Hade-haden sabulun:
Sabulun Zaitun, Tetmosol, sabulun salo da na gana, sabulun karas, sabulun kukumba, Kurkur (turmeric)
Yadda ake amfani:
Ki hada su su yi sabulu guda. Ki rika amfani da shi duk wanka. Zai tsabtace jiki, ya magance kuraje, ya hana duhu.
7. Hadin maganin kuraje
Abubuwan hadawa:
Zuma, ruwan khal, man zaitun
Yadda ake amfani:
A dafa su kadan a wuta, a kara ruwa, a juya sosai. Ki wanke fuskarki da sabulu, ki goge da auduga mai jika da wannan hadin. Yana kawar da kuraje da dattin fuska.
8. Steaming na fuska (Tururin Gyara Fuska)
Hadin farko:
Kwai, zuma, nono
Yadda ake amfani:
A hada a shafa a fuska, sannan a turara da ruwan zafi. Yana kashe kuraje.
Hadi na biyu:
Kindirmo (nono), man zaitun zuma
Yadda ake amfani:
A hada, a shafa a fuska, sannan a sa ruwa mai zafi a kwano, ki kara fuska a kai, ki lullube fuskar na minti 10 zuwa 15. Daga nan ki wanke da ruwan sanyi.
9. Domin hasken fata
Hadi na 1:
Itacen sandal wood, Kurkur, madara
Hadi na 2:
Kurkur, madara
Kwaiduwar kwai
Yadda ake amfani:
Ki shafa kafin wanka safe da yamma. Yana sa fata ta haskaka kamar zinariya.
10. Gyaran fuska mai tumbur
Abubuwan hadawa:
Ruwan kal (binegar) – cokali 10, man zaitun – cokali 2, zuma cokali 2, ruwa kadan
Yadda ake amfani:
A dora a wuta su dan yi zafi, ki kara ruwa kadan. Ki tsoma auduga ki rika goge fuska bayan kin wanke da sabulu. Yana cire duhu da tabo, ya sanya fuska ta yi fes.
Daga Sirrin Rike Miji
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp