Assalamu alaikum masu karatu, barkan mu da sake haduwa da ku a wannan makon a cikin shirin na mu mai farin jini da albarka na Adon Da Kwalliya.
A yau shafin na mu zai kawo muku yadda za ku gyara jikinku, Uwargida ko Amarya:
Gyara jiki
Fatar ta yi laushi da sheki
Ga abubuwan da za ku tanada
Man Zaitun, Lalle, Kurkur, Madara Peak
Za ku hade wadannan kayan hadin guri daya, sai ku kwaba su ku shafe jikinku da fuskarku, za ku yi wannan hadin kafin ku shiga wanka. Idan ya bushe a jikinku sai ku murje sannan sai ku shiga wanka jiki yana yin kyau ya yi sheki
Wani nau’in gyaran jikin
Wannan hadin shi ake cewa maida tsohuwa yarinya.
Kurkur, Dulka, Zuma, Kwai, Lemun tsami
Ki hade su guri dauya ki samu ki kwaba kamar yadda ake kwaba lalle, amma ya fi kwabin lalle ruwa, sai ki shafe a fuskarki, idan kuma har da jiki kike so, sai ki shafa har da jiki, bayan awa daya sai ki shiga wanka za ki ga yadda jikinki zai goge
Wani nau’in kuma
Fata ta yi laushi da sheki, lalle, Kwaiduwar Kwai guda, manja cokali 3 kur-kur.
Sai ki kwaba su guri daya ki shafe jikinki zuwa awa daya, sai ki yi wanka da ruwan zalla da ruwan dumi ki shafe jikinki da ita sai ki kuma yin wanka.
Kyan Fuska
Sai ki hade su guri daya ki kirba su cikin turmi, ki mulmula ki rinka wanke fuska za ki ga yadda fuskarki za ta yi