Assalamu alaikum masu karatu, barkanmu da sake haduwa da ku a wannan makon cikin shirin namu mai farin jini da albarka na Ado Da Kwalliya.
A yau shafin namu zai kawo muku yadda za ku gyara mamanku:
Domin matan da suka haifu kawai (mata masu Jego) ga wacce take bukatar mamanta ya ci gaba da zama a tsaye. Duk mace idon ta samu ciki jikinta kan canja za ku ga ta dan kunbura, har sai ta kai watanni shida zuwa bakwai da samun ciki kafin jikinta ya koma dai-dai.
Wata kan ma har sai ta haifu sannan take dawowa daidai, to haka nan abin yake a bangaren mama, da zaran mace ta samu ciki sai ku ga mamanta a watanni biyi zuwa uku ya kunboro ya ciko ya tsatstsaya sosai, fiye da yadda yake ada, to da zarar ta haifu kuma In aka samu ‘yan watanni tana shayarwa sai kaga har mamannata ya fara zubewa wato (Kwanciya) yana yin kasa, to ga wacce ba ta son mamanta ya zube bayan ta haifu, sai ta yi wannan abin da za mu fada na tsawon kwana 40.
Kayan da ake bukata: Aya bushasshiya, dabino wanda bai bushe ba, kwakwa, citta mai yatsu, kanunfari, masoro.
Sai ta rinka yin kunu (Kunun Aya) da su kullum tana sha kofi biyu, na tsawon kwana arba’in, za ta ga hatta jaririnta sai ya fi lafiya, kuma in ta gama wanka maigidonta ya sadu da ita zai jita tamkar ba ita bace wannan matar tasa da ya sani a baya, haka kuma mamanta zai ci gaba da zama a tsaye kamar ba wacce take shayarwa ba.
Amma akwai bukatar ta rinka maimatawa duk bayan wani Lokaci zuwa Lokaci, In Sha Allahu za ku ga biyan bukata.