Duk da cewa ba a kammala cimma matsaya ba a tattaunawar kasar Sin da Amurka kan alakarsu ta kasuwanci da tattalin arziki, amma sakamakon da ake samu a baya-bayan nan alama ce mai karfafa gwiwa ga al’ummomin duniya masu neman ganin an rage fargabar rashin tabbas da ake kaka-ni-ka-yi a ciki a fagen kasa da kasa. Kara wa’adin jingine karin haraji daga sassan biyu na tsawon kwanaki 90, ya sake farfado da fatan samun kwanciyar hankali mai inganci a fannin tattalin arziki tsakanin manyan kasashen biyu.
Kasashe da dama, wadanda suka tsinci kansu a tsaka-mai-wuya sakamakon tataburzar kasuwancin Sin da Amurka, sun jima suna kira ga bangarorin biyu da su kara kaimi. Abin da ake tsammani a bayyane yake: gudanar da dangantakar tattalin arziki tsakanin kasashen biyu bisa sauke nauyin da ya rataya a wuyar ko wane bangare, da nuna gaskiya, da hangen nesa. Duniya ta zuba ido tana jiran ganin samun kyakkyawan sakamako a tattaunawar kasashen biyu.
Sin da Amurka a matsayinsu na manyan kasashe biyu masu karfin tattalin arziki a duniya, su ne ginshikan cinikayya, da zuba jari, da kirkire-kirkiren sabbin fasahohi. Dangantakar tattalin arzikin kasashen biyu ba kawai tana shafar muradun cikin gidansu ba ne kawai, kanwa ce uwar-gami ga tabbatar da zaman lafiyar duniya. Don haka ne kasashe da dama, tun daga masu tasowa zuwa sauran kasashe masu karfin tattalin arziki, suka sa ido sosai tare da yin kira ga kasashen biyu da su dawo da tafiyar da harkokin tattalin arzikinsu cikin tsanaki da hangen nesa.
Dambarwar kasuwancin kasashen biyu ta haifar da rudani ga tsarin samar da kayayyaki a duniya, da masana’antu tun daga kan na kimiyya da fasaha musamman a bangaren na’urorin kera kayan laturoni na semiconductors, da kere-keren fasahar AI har zuwa kayan noma da sauran na amfanin yau da kullum. Kazalika, an shiga rashin tabbas a bangaren kasuwannin hannayen jari na duniya, da canjin kudi, da kuma sauye-sauyen ra’ayoyin masu saka jari.
Kamar yadda kasar Sin ta sha nanatawa, babu wanda zai yi nasara a yakin cinikayya da kasuwanci, kuma ya dace Amurka ta rika sauke nauyin dake wuyanta. Rura wutar yake-yaken kasuwanci da kakaba takunkumai, ba su da wata ma’ana sai tayar da zaune tsaye, da sabbaba tsadar kayayyaki, da haifar da koma bayan tattalin arziki. Duk da cewa, Sin ta fito baro-baro a fili ta shaida cewa ba ta tsoron gwabzawa, amma tana ci gaba da yekuwar tabbatar da damawa da kasashe daban-daban a harkokin duniya. Kasashen duniya sun amince da tsarin ciniki na duniya wanda ya dogara da ka’idojin dake karkashin kulawar hukumar kasuwanci ta duniya (WTO). Idan ma akwai wasu sauye-sauye na manufofi musamman a kan kayayyakin da ake fitarwa daga kasashe, kamata ya yi a tattauna a tsakani domin samun maslaha amma ba yin gaban-kai kamar yadda Amurka ke nunawa saboda rashin mafadi ba.
Muryoyi daga ko’ina cikin duniya sun nemi a warware matsalar bisa turbar adalci. Shugabannin tarayyar Turai sun yi ta kira ga kasashen Sin da Amurka da su kiyaye bude kasuwanni da gudanar da gasa ta gaskiya. Kasashen kudu maso gabashin Asiya, sun ba da shawarar tabbatar da kwanciyar hankali. Kasashen Afirka da na Latin Amurka sun nuna damuwa da halin da ake ciki saboda barazanar da lamarin yake yi ga damarmakin zuba jari da kasuwancin kasashensu.
Gyaruwar dangantakar tattalin arziki tsakanin Sin da Amurka za ta iya haifar da wani sabon zamani na hadin gwiwa, da kirkire-kirkire, da ci gaban da ya kunshi kasashen duniya baki daya. A wannan duniyar tamu wadda bukatar hada hannu da juna ke kara bayyana, kiran a bayyane yake, wato duniya tana bukatar Sin da Amurka ba kawai don zama tare ba, har ma su zama ababen buga misali a bangaren aiki tare. (Abdulrazaq Yahuza Jere)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp