A wani mataki na inganta tattalin arziki musamman fitar da kayayyaki zuwa kasashen waje, gwamnan jihar Yobe, Mai Mala Buni, ya mika takardar shedar mallakar fili mai fadin hekta 300 ga hukumar da ke sarrafa kayayyakin da ake fitarwa a Nijeriya (NEPZA) domin tallafawa ayyukanta a jihar.
Wata sanarwa da babban daraktan hulda da manema labarai da yada labarai na Gwamnan ya fitar, Alhaji Mamman Mohammed, ta ce Buni a lokacin da yake mika takardun shaidar mallakar filin ga babban daraktan ciniki da saka hannun jari na hukumar, Alhaji Usman Bakori, gwamnan ya bukaci hukumar ta yi amfani da filin yadda ya kamata.
- An Juya Bangare Na Karshe Na Gadar Titi Mafi Tsawo Dake Saman Layin Dogo A Kasar Sin
- Kotu Ta Dakatar da JAMB Daga Hana Ɗalibai Ƴan Ƙasa Da Shekaru 16 Shiga Jami’a
Gwamnan ya bayyana cewa, ”Ya kamata ku tabbatar da fara amfani da filin cikin sauri don bunkasa ci gaban tattalin arzikin jihar.
“Gwamnati ta ware filin ne a kusa da tashar dakon kaya domin bunkasa harkokin kasuwanci a jihar,” in ji shi.
Gwamna Buni ya kara da cewa, gwamnati za ta ci gaba da bai wa hukumar da sauran abokan huldar hadin gwiwa don hanzarta ganin an samu ci gaba a jihar.