An zabi Erling Haaland a matsayin Gwarzon dan wasan Duniya na BBC na shekarar 2023 bayan ya taimaka wa Manchester City ta samu nasarar lashe gasar zakarun Turai.
Dan Kasar Norway, mai shekara 23, ya zura kwallaye 52 a dukkan wasannin da City ta lashe a gasar Premier da gasar Zakarun Turai da kuma gasar cin kofin FA a kakar 2022 zuwa 23.
- Rikicin Siyasar Jihar Ribas: Dattawa Da Kabilar Ijaw Sun Yi Fatali Da Sabon Sulhu Bisa Zargin Kashin Dankali
- Wakilin Sin: Ya Dace A Daidaita Batun Kiyaye Zaman Lafiya Na AU Ta Hanyoyin Afirka
Babu wani dan wasa da ya taba zura kwallaye a Kulob din Premier a cikin kaka daya kamar yadda Haaland ya zura a kakar wasan da ta gabata.
Haaland ya lashe kyautar takalmin zinare na gasar Premier a kakar wasa ta 2022 zuwa 23 inda ya zura kwallaye 36 a wasanni 38.
“Na gode da kuka zabe ni a matsayin gwarzon dan wasan duniya na BBC, domin a kakar da ta gabata na samu nasarori da dama,” in ji Haaland