• English
  • Business News
Sunday, October 26, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Hada-hadar Tattalin Arzikin Sin Ta Gudana Bisa Daidaito A Watan Mayu

by CGTN Hausa and Sulaiman
4 months ago
Sin

Hukumar kididdiga ta kasar Sin, ta fitar da wasu alkaluma a Litinin din nan, dake shaida gudanar hada-hadar tattalin arzikin kasar bisa daidaito a watan Mayun da ya gabata. Alkaluman da hukumar ta fitar yayin taron manema labarai, sun nuna ci gaban da aka samu a watan na Mayu, duk kuwa da matsin da aka fuskanta.

Hukumar ta ce an samu daidaito a karuwar samar da hajojin masana’atu, da fadadar bukatunsu, da guraben ayyukan yi, kana an samu ci gaba mai inganci dake kara kusantar managarcin ci gaba da kirkire-kirkire.

Kazalila, alkaluman sun shaida yadda sashen masana’antun sarrafa hajoji ke kara bunkasa bisa daidaito, inda sashen sarrafa manyan kayayyakin aiki, da na masana’antun fasahohin zamani ke kara fadada cikin sauri. Bugu da kari, kasar Sin ta samu ci gaba a fannin sana’o’in samar da hidimomi. Inda a watan na Mayu, alkaluman ci gaban sana’o’in samar da hidimomin ya karu da kaso 6.2 bisa dari a mizanin shekara-shekara, wato an samu karin saurin kaso 0.2 bisa dari sama da wanda aka gani a watan Afirilu.

A daya bangaren kuma, yanayin sayayya ya farfado sosai, yayin da aka samu karuwar musayar sabbi da tsofaffin kayayyaki bisa rangwamen da gwamnati ta samar. Kana darajar sayayyar daidaikun kayayyakin bukatun yau da kullum ta kai kudin Sin yuan biliyan 4,132.6, karuwar da ta kai ta kaso 6.4 bida dari a mizanin shekara-shekara. (Saminu Alhassan)

LABARAI MASU NASABA

An Yi Liyafar Murnar Kebe Ranar Tunawa Da Kawo Karshen Mulkin Mallakar Japan A Yankin Taiwan

Sin Da Amurka Sun Fara Tattaunawa Kan Tattalin arziki Da Cinikayya A Kuala Lumpur

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

An Yi Liyafar Murnar Kebe Ranar Tunawa Da Kawo Karshen Mulkin Mallakar Japan A Yankin Taiwan
Daga Birnin Sin

An Yi Liyafar Murnar Kebe Ranar Tunawa Da Kawo Karshen Mulkin Mallakar Japan A Yankin Taiwan

October 25, 2025
Sin Da Amurka Sun Fara Tattaunawa Kan Tattalin arziki Da Cinikayya A Kuala Lumpur
Daga Birnin Sin

Sin Da Amurka Sun Fara Tattaunawa Kan Tattalin arziki Da Cinikayya A Kuala Lumpur

October 25, 2025
Firaministan Sin Ya Isa Singapore Don Ziyarar Aiki
Daga Birnin Sin

Firaministan Sin Ya Isa Singapore Don Ziyarar Aiki

October 25, 2025
Next Post
‘Yansanda Sun Kama Matasa 51 da Ake Zargi Da Faɗan Daba A Kano

‘Yansanda Sun Kama Matasa 51 da Ake Zargi Da Faɗan Daba A Kano

LABARAI MASU NASABA

An Yi Liyafar Murnar Kebe Ranar Tunawa Da Kawo Karshen Mulkin Mallakar Japan A Yankin Taiwan

An Yi Liyafar Murnar Kebe Ranar Tunawa Da Kawo Karshen Mulkin Mallakar Japan A Yankin Taiwan

October 25, 2025

Nafisa Abdullahi Aminu: Yarinyar Da Ta Ɗaukaka Darajar Nijeriya A Idon Duniya

October 25, 2025
Sin Da Amurka Sun Fara Tattaunawa Kan Tattalin arziki Da Cinikayya A Kuala Lumpur

Sin Da Amurka Sun Fara Tattaunawa Kan Tattalin arziki Da Cinikayya A Kuala Lumpur

October 25, 2025
Gwarzon Gwamnan 2025, Biodun Abayomi Oyebanji

Gwarzon Banki Na Shekarar 2025 Bankin Providus

October 25, 2025
Firaministan Sin Ya Isa Singapore Don Ziyarar Aiki

Firaministan Sin Ya Isa Singapore Don Ziyarar Aiki

October 25, 2025
Gwarzuwar Hukumar Da Ta Kawo Sauyi A Kula Da Muhalli A 2025 Hukumar NASENI

Gwarzuwar Hukumar Da Ta Kawo Sauyi A Kula Da Muhalli A 2025 Hukumar NASENI

October 25, 2025
An Gudanar Da Taron Cika Shekaru 80 Da Kawo Karshen Mulkin Mallakar Japan A Yankin Taiwan Da Dawo Da Shi Kasar Sin A Beijing

An Gudanar Da Taron Cika Shekaru 80 Da Kawo Karshen Mulkin Mallakar Japan A Yankin Taiwan Da Dawo Da Shi Kasar Sin A Beijing

October 25, 2025

Daɓid Adeyemi

October 25, 2025
Wakilin Sin: Shawarar GGI Ta Nuna Yadda Za A Jagoranci Bunkasa Makomar MDD

Wakilin Sin: Shawarar GGI Ta Nuna Yadda Za A Jagoranci Bunkasa Makomar MDD

October 25, 2025
Gwarzuwar Ma’aikaciyar Jinya Ta Shekarar 2025: Misis Mabel Ijeoma Duaka

Gwarzuwar Ma’aikaciyar Jinya Ta Shekarar 2025: Misis Mabel Ijeoma Duaka

October 25, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.