• English
  • Business News
Friday, November 7, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Hada Kai Ba Hada Baki Ba Ne…

by CMG Hausa
2 years ago

A makon da ya gabata ne, firaministan kasar Sin Li Qiang, ya kammala ziyarar da ya kai kasashen Jamus, da Faransa, ziyarar dake da babbar ma’ana ga bangarorin biyu. A yayin wannan ziyara mai muhimmanci a wannan lokaci da duniya ke fama da rashin tabbas, jami’in na kasar Sin ya gana da wakilan kasashen biyu a fannin siyasa, da masana’antu, da kasuwanci, inda ya jadadda yadda bunkasuwar kasar Sin ta kawowa duniya damammaki maimakon hadari.

A duk inda Li Qiang ya ziyarta, ya kan jaddada matsayin kasarsa na mutunta juna da samun nasarar moriyar juna da hada kai don samun zaman lafiya da kwanciyar hankali da ma wadata a fadin duniya.

  • Jagororin ’Yan Kasuwa Sun Bayyana Kwarin Gwiwa Ga Ci Gaban Tattalin Arzikin Kasar Sin Yayin Taron Davos

Su ma shugabannin kasashen biyu sun bayyana matsayin da suke kai na nuna adawa da ra’ayin katse huldar bangarorin biyu, da ma yaki da ko wane irin mataki na jayayya da juna, ko mayar da wani bangare saniyar ware. Sun kuma bayyana cewa, Sin da Turai na da matsaya daya game da kin katse huldarsu, da ingiza hadin kai, da samarwa duniya tabbaci bisa hali mai sarkakiya da duniyar ke ciki. Wannan ya kara nuna cewa, ra’ayin bangarorin ya zo daya, matakin dake nuna cewa, duk mai neman illata wannan alaka ba zai taba yin nasara ba.

Idan ba a manta ba, tun daga karshen shekarar da ta gabata ce, shugabannin Sin da Turai ke kara yaukaka mu’ammala, da tuntubar juna, inda shugaban gwamnatin kasar Jamus Olaf Scholz, da shugaban kasar Faransa Emmanuel Macron da sauran shugabannin kasashen Turai, suka ziyarci kasar Sin, tare da cimma matsaya daya bi da bi da shugaban Sin, kan yadda za su zurfafa dangantaka da hadin kansu.

Ziyarar Li Qiang ta wannan karo a Turai, na da zummar tabbatar da matsaya daya da aka cimma, da ingiza hadin kansu a fannoni daban daban. Ai dama hadin kai ba wai hada baki ba ne. Kuma da abokin daka ake shan gari. (Ibrahim Yaya)

LABARAI MASU NASABA

An Kaddamar Da Taron Kolin Wuzhen Na Ayyuka Masu Nasaba Da Yanar Gizo

Sin Ta Kadammar Da Babban Jirgin Ruwan Dakon Jiragen Yaki Na CNS Fujian a Rundunar Sojan Ruwanta

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

An Kaddamar Da Taron Kolin Wuzhen Na Ayyuka Masu Nasaba Da Yanar Gizo
Daga Birnin Sin

An Kaddamar Da Taron Kolin Wuzhen Na Ayyuka Masu Nasaba Da Yanar Gizo

November 7, 2025
Sin Ta Kadammar Da Babban Jirgin Ruwan Dakon Jiragen Yaki Na CNS Fujian a Rundunar Sojan Ruwanta
Daga Birnin Sin

Sin Ta Kadammar Da Babban Jirgin Ruwan Dakon Jiragen Yaki Na CNS Fujian a Rundunar Sojan Ruwanta

November 7, 2025
Xi Jinping Ya Taya Paul Biya Murnar Tazarce a Kamaru
Daga Birnin Sin

Xi Jinping Ya Taya Paul Biya Murnar Tazarce a Kamaru

November 7, 2025
Next Post
Gidan Yari Da Ya Saba Doka Da Amurka Ta Kafa Misali Ne Na Take Hakkin Doka Da ‘Yancin Dan Adam

Gidan Yari Da Ya Saba Doka Da Amurka Ta Kafa Misali Ne Na Take Hakkin Doka Da 'Yancin Dan Adam

LABARAI MASU NASABA

Jerin Gwarazan Taurarinmu!

Jerin Gwarazan Taurarinmu!

November 7, 2025
‘Yansanda Sun Kama ‘Yan Ƙungiyar Asiri 4, Sun Ƙwato Makamai A Filato

Zaben Kananan Hukumomi A Neja Ya Bar Baya Da Kura

November 7, 2025
Gwamnatin Zamfara Ta Ɗauki Malaman Makaranta 500 Aiki

Gwamnatin Zamfara Ta Ɗauki Malaman Makaranta 500 Aiki

November 7, 2025
GORON JUMA’A

GORON JUMA’A

November 7, 2025
Majalisar Wakilai Ta Yi Tir Da Harin Da Aka Kai Wa Tawagar Ɗan Majalisar Neja

Majalisar Wakilai Ta Yi Tir Da Harin Da Aka Kai Wa Tawagar Ɗan Majalisar Neja

November 7, 2025
Yadda Duniya Ta Fara Wayewa Tun Daga Zamanin Annabi Nuhu (AS) Har Manzon Allah (SAW) Ya Zo Ya Cika Komai (2)

Yadda Duniya Ta Fara Wayewa Tun Daga Zamanin Annabi Nuhu (AS) Har Manzon Allah (SAW) Ya Zo Ya Cika Komai (2)

November 7, 2025
Yaduwar Juyin Mulki A Afirka

Yaduwar Juyin Mulki A Afirka

November 7, 2025
Rashin Daukar Tsauraran Matakai Na Iya Durkusar Da Bangaren Noma – Shehu Galadima

Hanyoyin Noma Na Gargajiya Ba Za Su Iya Wadata Abinci A Nijeriya Ba -Masanin Kimiyya

November 7, 2025
An Kaddamar Da Taron Kolin Wuzhen Na Ayyuka Masu Nasaba Da Yanar Gizo

An Kaddamar Da Taron Kolin Wuzhen Na Ayyuka Masu Nasaba Da Yanar Gizo

November 7, 2025
Hajjin 2026: NAHCON Ta Kammala Tantance Masaukai Da Ɗakunan Dafa Abincin Alhazai A Madinah

Hajjin 2026: NAHCON Ta Kammala Tantance Masaukai Da Ɗakunan Dafa Abincin Alhazai A Madinah

November 7, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.