• English
  • Business News
Sunday, October 19, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Hadadden Gashin Kifi

by Bilkisu Kassim
2 years ago
Kifi

Assalamu alaikum masu karatu barkammu da sake haduwa da ku a wannan makon a cikin shirin na mu na Girki Adon Mata.

Abubuwa da Uwargida za ta tanada:

Kifi, fafirika, fulawa, kwai, yis, mai, albasa, magi, gishiri, kayan kamshi:

Da farko za ki wanke kifin sannan sai ki yi kamar ganishin dinshi wato za ki dan tsatstsaga tsakiyar sa kadan-kadan saboda kayan hadin ya shiga cikinsa, sai ki dan barbada  masa fafirikan sannan ki dan barbada masa magi da gishiri da kayan kamshi sai ki shashshafa a jikin kifin, sannan ki juya kasan shima ki shashshafa ko ina ya zama ya samu ya shisshiga cikin kifin inda kika tsatstsaga sai ki yanka albasa kanana ki barbada a saman kifin sannan sai ki dan barbada mai a sama, sai ki sashi a obon ki kunnan masa wuta ki barshi ya kasu kafin ya kasu sai ki kwaba fulawa, idan kika zuba fulawar a wata roba sai ki zuba yis sannan ki zuba gishiri sannan ki kawo dan mai ki zuba, ki zuba ruwa  mai dan dumi ki kwaba, za ki kwaba da dan tauri  kamar kwabin cincin sai kibarshi ya yi kamar minti goma saboda ya dan tashi kafin nan kifin ya gasu, sai ki fitar da kifin ki barshi yadan huce.

Daga nan ki dakko wannan kwabin fulawar, ki samu cafin bot sai ki dan barbada fulawa a samansa sannan ki raba wannan kwabin naki biyu sai ki dora daya akan cafin bot din ki tada shi daidai yadda za ki rufa a saman kifin sai ki dakko dayan shima ki tada shi kamar yadda kika tada dayan sai ki daga wannan kifin ki dora shi akan guda daya, dayan kuma ki rufa shi a saman kin ga kin rufe kifin, sai ki kama bakin na kasa da na sama ki rurrufe shi ki mammane shi ko ina ya rufe haka za ki gewaye shi tun da kifin yana ciki kuma ya rufe shi gaba daya.

LABARAI MASU NASABA

Yadda Ake Alkaki

Yadda Ake Gurasa Ta Semovita

Sannan ki fasa kwai ki dan sa masa gishiri kadan sai ki shafe shi da kwan ki maida shi cikin obon ki kunna wutar sama da kasa ya kasu. Habba mana Uwargida ya kika ga kifin nan ranar mai gida babu futa hira.

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

Yadda Ake Alkaki
Girke-Girke

Yadda Ake Alkaki

October 19, 2025
Yadda Ake Gurasa Ta Semovita
Girke-Girke

Yadda Ake Gurasa Ta Semovita

October 12, 2025
Yadda Ake Lemon Tsamiya (Tamarin Juice)
Girke-Girke

Yadda Ake Lemon Tsamiya (Tamarin Juice)

October 4, 2025
Next Post
An Tsayar Da Ranar Da Za A Fara Buga Firimiyar Nijeriya

An Tsayar Da Ranar Da Za A Fara Buga Firimiyar Nijeriya

LABARAI MASU NASABA

Ko Kin San… Yadda Za Ki Gyara Kanki Da Kanki?

Ko Kin San… Maganin Sanyi Na Mata (Infection)?

October 19, 2025
JTF Ta Kama Wani Da Ake Zargin Mai Safarar Miyagun Ƙwayoyi Ne Ga ‘Yan Bindiga A Jihar Kogi

JTF Ta Kama Wani Da Ake Zargin Mai Safarar Miyagun Ƙwayoyi Ne Ga ‘Yan Bindiga A Jihar Kogi

October 19, 2025
Abin Da Nijeriya Ke Bukata Kafin Samun Damar Zuwa Gasar Kofin Duniya

Abin Da Nijeriya Ke Bukata Kafin Samun Damar Zuwa Gasar Kofin Duniya

October 19, 2025
Yadda Ake Alkaki

Yadda Ake Alkaki

October 19, 2025
Kar Ki Yi Kuskuren Da Za Ki Yi Da Na Sani A Kai (1)

Kar Ki Yi Kuskuren Da Za Ki Yi Da Na Sani A Kai (2)

October 19, 2025
An Sanya Hannu Kan Yarjejiyar Zaman Lafiya A Gaza

An Sanya Hannu Kan Yarjejiyar Zaman Lafiya A Gaza

October 19, 2025
Nijar

Gwamnatin Nijar Ta Yaye Tsofaffin Mayaka 369 Da Aka Bai Wa Horon Sauya Tunani

October 19, 2025
Yadda Zargin Takardar Karatun Bogi Ta Tilasta Wa Minista Nnaji Murabus

‘Yan Siyasa 11 Da Suka Faɗa Dambarwar Takardar Shaidar Karatu Ta Bogi

October 19, 2025
gombe

Ɗaliban Jihar Gombe Sun Samu Ƙarin Kashi 100 Na Kuɗin Tallafin Karatu

October 18, 2025
Ɗaliban Fasaha Sun Ɓullo Da Dabarar Tsaro Ta Harkar Noma

Ɗaliban Fasaha Sun Ɓullo Da Dabarar Tsaro Ta Harkar Noma

October 18, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.