• English
  • Business News
Friday, July 11, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Hadarin Da Ke Kunshe Da Jin Bangare Daya Na Labari

by Azu Ishiekwene
4 hours ago
in Bakon Marubuci
0
Hadarin Da Ke Kunshe Da Jin Bangare Daya Na Labari
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsAppTelegram

Akwai wani bangare na aikina da zai iya hadiye baki-daya. An tarbiyantar da ‘yan jarida, wajen neman abincin da manyan kayan hadinsa sun kunshi aikata laifuka da gangan, abin da ya shafi tsakanin namiji da mace da kuma kudi. Komai kuwa bayan wannan, ajiye shi a gefe ake yi. Shi yasa, idan ka bibiyi abubuwan da ake karantawa a jaridu, rediyo, talabijin ko kuma abubuwan da ake yadawa a kafafen yada labarai na intanet, wani lokaci sai ka yi tunanin cewa; kamar ana daf da fara tura duniya wilbaro.   

Daga rahotannin masu tayar da hankali na kashe-kashen Jihohin Benuwai da Filato zuwa labaran sace-sacen mutane don neman kudin fansa, sauran ayyukan ta’addanci da kananan laifuka; ba a samu sauki daga wadannan munanan labaru ba. Haka zalika, tun daga yakin Ukraine har zuwa barnar da aka yi a Gabas ta Tsakiya da Tekun Fasha, labaran babu dadin ji.

  • Ƴan Bindiga Sun Yi Wa Jami’an NSCDC Ƙwantan Ɓauna A Binuwe
  • Majalisar Ta Kwace Shugabacin Kwamitin Da Natasha Ke Jagoranta

Labari mara kyau yana da dadin ji?

Ba don dabi’ar yawaitar munanan labarai daga ‘yan siyasa da sauran abokan huldodinsu ba, da rahotannin da ‘yan jarida ke fitarwa ba zai taba zama mummuna ko maras dadi ba.

Rikici ya dabaibaye babbar jam’iyyar adawa ta Nijeriya, PDP, jam’iyyar LP, ita ma ta shiga rudani. Jam’iyyar SDP, cikin tsaka mai wuya. Haka nan, wani juyin mulki ya hambarar da shugaban jam’iyyar APC mai mulki da rana tsaka, sannan kuma ana shirin kafa jam’iyyar hadin gwiwa da ke fuskanta hada kwanji da jam’iyya mai mulki.

Labarai Masu Nasaba

Yawaitar Al’umma: Martanin Karl Marx Ga Rabaran Malthus

Dabi’a: Yadda Ake Gini Da Rusa Ta 

 

A daya bangaren kuma

Fita zuwa wani yanki daban da ba naka a halin yanzu, yana da nasa fa’idar. Domin kuwa, na ziyarci wasu jihohi uku kwanan nan; wadanda labarai a kansu babu dadin ji. Jihohin su ne, Delta, Inugu da kuma Zamfara, wadanda galibi labaransu marasa dadi ne ta fuskar siyasa, ta’addanci da sauran munanan laifuka. Daga labarun da ake samu yau da kullum, za ka yi tsammanin cewa; wadannan jihohi tuni sun tashi daga aiki, amma daga ziyarar da na kai musu; na ga abubuwan ban mamaki, tsoratarwa da kuma hadari duk da ke dauke cikin wannan labari.

Duk da cewa, kowace jiha akwai abubuwan da ta fi bai wa muhimmanci, su ma kamar sauran jihohin; suna fuskantar kalubale na yi wa al’umma aiki ta hanyar samar da damammaki, rage talauci da kuma tsantseni wajen sarrafa dukiyar al’umma.

Duk da cewa, har yanzu akwai sauran rina a kaba, amma abin da na gani a dan wannan lokaci da na ziyarci wadannan jihohi uku, tattakina zuwa Jihar Zamfara; shi ne mafi matukar tsoro a wajena

 

Zuwa Gusau

A karon farko da aka gayyace ni zuwa babban birnin jihar, Gusau, sai na yi watsi da tafiyar. Domin kuwa, a tafiya irin wannan akwai bukatar yin tunani da nazari mai zurfin gaske, musamman ganin yadda nake samun munanan labarai a kan Ado Aliero da sauran tawagarsa ta ‘yan ta’adda da ke yankin.

Har ila yau, sai aka sake turo min da wata gayyatar. Amma dai, a wannan karon akwai dan kwarin gwiwa, musamman ganin cikin tawagar da zan bi na tattaunawa ta farko da za a yi da Gwamna Dauda Lawal kai tsaye a kan wa’adin shekaru biyu da ya kwashe kan mulki. Tawagar ta kunshi; Gbenga Aruleba daga gidan talajin na AIT, Reuben Abati, ARISE TB da matarsa, Kiki, sai Ahmed Shekarau daga Media TRUST, Onuoha Ukeh daga SUN da kuma Babajide Otitoju, wanda Olajumoke Olatunji ya maye gurbinsa daga TBC.

 

ChatGPT da Gusau

Amma fa akwai matsala. Ta yaya za mu isa Gasau, duk da sanin abin da muka sani, na tambayi ‘ChatGPT’. Sai amsa min da cewa, kada ku tafi idan har tafiyar ba mai muhimmanci ba ce.

Ya ba da sanarwar tafiye-tafiye daga ofishin harkokin waje na burtaniya, Australia, Canada da kuma Amurka tare da gargadi game da tafiye-tafiye saboda tashin hankali, ta’addanci da kuma garkuwa da mutane, yana mai bayyana cewa; “Babbar matsaya daga hukumomin kula da tafiye-tafiye, ba ta ba da shawarar yin tattaki zuwa Jihar Zamfara, idan har ba akwai bukatar yin hakan ba.

“Titin Zariya zuwa Zamfara, musamman Funtua da ke Jihar Katsina, Tsafe, Maru-Dansadau, an bayyana su a matsayin wasu yankuna na mutuwa, wato wani filin wasa ne na Dogo Gide da Bello Turji, wanda tawagarsu ta ‘yan ta’adda suka kashe matafiya akalla 20, kamar yadda rahoton AP ya bayyana a watan Afrilun wannan shekara. Ina kan hanya, amma na kudiri niyyar tafiya.

 

Mutuwa da dawowa

Na yi ta mutuwa ina dawowa a cikin awa biyu da minti sha biyar, tsoro ya gama kama ni tare da alhinin cewa; idan na mutu a shekara 60, ba wai na mutu da kuruciya ba ne. Ban san cewa, matata ta lallaba ta sanya min wani abin kariya a cikin wata ‘yar karamar kwalba.

Gaba-daya ban lura ba, sai da na dawo daga tafiyar ina goge jakata, wannan ya isa ta bugi kirji da cewa; ta taimaka min da wani sirri na kariya. Na kasance a ankare cikin tsawon wannan tafiya ta kimanin kilomita 450 daga Abuja, cike da dimuwa.

Abin da ya ba ni mamaki, titin da ke tsakanin Zaiya da Katsina, mai layi biyu ne, sannan kuma yana da kyau sosai; titin bai tsuke ba sai da muka shiga Katsina, kana kuma ya sake bude bayan mun yi nisa ga duwatsu masu ban sha’awa da tsaunika da dukkanin bangarorin titin biyu. Amma titin Abuja zuwa Kaduna, abin kunya ne idan aka kwatanta shi da wannan, amma duk da haka; babban titin Abuja zuwa Kadunan ya lalace, kai ka ce shi ne kofar shiga Arewa Maso Yamma.

 

Fargaba da dimuwa…

Bayan Zariya, a wasu lokuta, mun wuce garuruwa masu yawan jama’a, amma mafi shahara a cikinsu shi ne garin Funtua, garin wasu daga cikin jiga-jigan ‘yan siyasa da suka hada da marigayi Malam Ismail Funtua da kuma fitaccen dan kasuwa, Umaru Mutallab.

Kowa ya yi tsit, kuma na kasa tambayar kaina cewa; ko mutanen da ke zaune a kauyukan da kananan garuwan da muke ratsawa, sun san abin da ake fada game da su kafafen yada labarai? Yayin da muka shiga Tsafe, garin daya daga cikin manyan ‘yan ta’addan da suka yi kaurin suna wajen garkuwa da mutane, wadanda suka samu nasarar share wajen zama a Jihar Katsina kafin ziyarar tamu, duk gashin da ke jikina sai da ya tashi.

Duk da cewa, mun samu rakiyar jami’an ‘yansanda ga kuma shingayen sojoji da dama a hanyar, yayin da muka isa Tsafe, kilomita 48 zuwa Gusau, ba ku ga irin tsoro da firgicin da ke cikin motarmu ba. shiru kake ji kowa ya yi dif.

Bayan Tsafe, na yi zaton tashin hankali ya kare a wannan tafiya. Sai kuma na ji na samu sauki tare kuma da shiga rudani da muka shiga Gusau. Saukin shi ne da muka isa lafiya, rudanin kuma saboda titi mai hannu biyu da ake dab da kammala, wanda ya hade da na Zamfara mai tattare da hadari da ban tsoro a tare da shi.

 

An samu canji

Ashe da rabon zan ga irin wadannan al’amuran a Enugu, inda rabo da zuwa tun

2006 (lokacin Chimaroke Nnamani yana gwamna). Ziyarar da na yi zuwa Zamfara na yi ta tun a farkon shekarun 1990, lokacin tana hade da Jihar Sakkwato

 

Jiha

Bayan wani Kantoman Mulkin Soji daya, da kuma wasu gwamnonin farar hula hudu, kafin Dauda, na biyar, Zamfara ta kasance wani abu kamar tallan shirin wasan kwaikwayo na Kannywood, inda ‘yan siyasa ke kwashe dukiyar kasa, ciki har da jama’arta, tare da nuna iko ko shakka babu Dauda zai iya nuna bambanci a wannan tsari. A cikin shekaru biyu, ya inganta asibitocin tuntuba da ke Gusau zuwa asibitin koyarwa mai dauke da wasu kayan aiki na zamani, ya kuma inganta harkar samar da ruwan sha, sannan ya kawar da koma bayan kudin WAEC da NECO na dalibai, lamarin da ya sa jihar ta kasance da ta samu kyakkyawan sakamako na tsawon shekaru. Haka kuma ya gina sabon filin jirgin sama wanda za a iya budewa kafin Satumba.

Gwamnati ta ce ta biya basussukan gratuti da kuma fansho ga ma’aikatan kananan hukumomi da na jiha tun daga shekarar 2011, da aka kiyasta kudin sun kai Naira biliyan 13.6, baya ga biyan bashin albashin watanni hudu da ya gada tare da kara mafi karancin albashi daga Naira 7,000 duk wata zuwa Naira 70,000.

 

“Komawar harkoki”

A lokacin da ake tattaunawar kai tsaye da Abati ya tambayi Dauda yadda ya sanya jihar a kan turba mai ban sha’awa, ciki har da ba ta wutar lantarki ta farko tun bayan da aka kirkiro ta shekaru 29 da suka gabata, gwamnan ya ce hakan ya faru ne ta hanyar toshe leken asiri ta hanyar amfani da fasaha, da kuma ba da fifiko wajen bunkasa albarkatun jama’a da kuma inganta karfinsu.

Ya ce an kuma yi amfani da fasaha don tattarawa da yin amfani da bayanan sirri don gina jiha mafi aminci, yana mai shan alwashin cewa ba za ai yi sulhu da ‘yan fashi da masu laifi ba.

Idan rayuwar dare ta daidaita a Gusau, babu shakka dukkan jama’ar da suka rasa matsugunai da wuraren sana’a za su dawo inda suke musamman gonaki a hankali. Wannan kuma wani hangen nesa ne da mutum zai iya duba jihar da aka ayyana kusan shekaru talatin ta hanyar cusa tsattsauran ra’ayi na addini, sata da kuma ‘yan fashi.

Ishiekwene Babban Editan LEADERSHIP kuma mai Rubuce-rubuce a Kafofin watsa labarai da harkokin Kudi.


Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

Tags: Labari
ShareTweetSendShare
Previous Post

NPA Ta Yi Wa Ma’aikatanta 1,500 Karin Girma

Next Post

Bafarawa Ya Kaddamar Da Kungiyar Hada Kan Arewa Da Samar Da Zaman lafiya A Kaduna 

Related

Yawaitar Al’umma: Martanin Karl Marx Ga Rabaran Malthus
Bakon Marubuci

Yawaitar Al’umma: Martanin Karl Marx Ga Rabaran Malthus

7 days ago
Dabi’a: Yadda Ake Gini Da Rusa Ta 
Bakon Marubuci

Dabi’a: Yadda Ake Gini Da Rusa Ta 

4 weeks ago
SULEJA – An Ci Moriyar Ganga (3)
Bakon Marubuci

SULEJA – An Ci Moriyar Ganga (3)

1 month ago
SULEJA – An Ci Moriyar Ganga (2)
Bakon Marubuci

SULEJA – An Ci Moriyar Ganga (2)

2 months ago
Ta Ya Ake Gudanar Da Nagartacciyar Rayuwa?
Bakon Marubuci

Ta Ya Ake Gudanar Da Nagartacciyar Rayuwa?

3 months ago
Waraka Daga Bashin Ketare
Bakon Marubuci

Waraka Daga Bashin Ketare

3 months ago
Next Post
Bafarawa Ya Kaddamar Da Kungiyar Hada Kan Arewa Da Samar Da Zaman lafiya A Kaduna 

Bafarawa Ya Kaddamar Da Kungiyar Hada Kan Arewa Da Samar Da Zaman lafiya A Kaduna 

LABARAI MASU NASABA

Shafin Yanar Gizo Na ADC Ya Tsaya Cak Saboda Ɗumbin Magoya Baya Masu Son Yin Rijista

Shugabannin Jam’iyyar ADC Na Jihohi 36 Da Abuja Sun Bayyana Goyon Bayansu Ga David Mark

July 11, 2025
Gwamnan Zamfara Ya Raba Buhunan Taki 59,205 Ga Manoman Jihar

Gwamnan Zamfara Ya Raba Buhunan Taki 59,205 Ga Manoman Jihar

July 11, 2025
Matatun Man Fetur Na Nijeriya Ba Za Su Ci Gaba Da Aiki Yadda Ya Kamata Ba – Dangote

Matatun Man Fetur Na Nijeriya Ba Za Su Ci Gaba Da Aiki Yadda Ya Kamata Ba – Dangote

July 11, 2025
Sojoji Sun Kashe ‘Yan Bindiga Tare Da Kwato Makamai A Jihar Filato

‘Yan Bindiga Sun Kai Wa ‘Yansanda Hari Tare Da Kashe Wani Mutum Da Raunata Wani A Nasarawa

July 11, 2025
Goron Sallah

GORON JUMA’A

July 11, 2025
An Koka Kan Yadda Tsafi Da Jariran Da Aka Haifa Da Tsagaggen Lebe Ke Karuwa

An Koka Kan Yadda Tsafi Da Jariran Da Aka Haifa Da Tsagaggen Lebe Ke Karuwa

July 11, 2025
Bafarawa Ya Kaddamar Da Kungiyar Hada Kan Arewa Da Samar Da Zaman lafiya A Kaduna 

Bafarawa Ya Kaddamar Da Kungiyar Hada Kan Arewa Da Samar Da Zaman lafiya A Kaduna 

July 11, 2025
Hadarin Da Ke Kunshe Da Jin Bangare Daya Na Labari

Hadarin Da Ke Kunshe Da Jin Bangare Daya Na Labari

July 11, 2025
NPA Ta Yi Wa Ma’aikatanta 1,500 Karin Girma

NPA Ta Yi Wa Ma’aikatanta 1,500 Karin Girma

July 11, 2025
Shirin Sabunta Fata Na Tinubu Yana Samar da Damarmakin Cigaba — Minista

Shirin Sabunta Fata Na Tinubu Yana Samar da Damarmakin Cigaba — Minista

July 11, 2025
Talla

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In

Add New Playlist

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.