Abdullahi Tanko Yakasai, Babban Hadimi na Musamman ga Shugaban Kasa Bola Tinubu kan mu’amala da Jama’a a Arewa maso Yamma, ya raba kayayyakin makaranta da kayan koyarwa da kuma littafai ga daliban Kano 400.
A ranar Talata ne ya raba kayayyakin ga daliban makarantar firamare ta unguwar Rimi da ke unguwar Yakasai kwatas, Kano. Ya yi kira ga daidaikun jama’a da kungiyoyi da su bayar da tasu gudummawar wajen bunkasa ilimi musamman a matakin farko.
Ya koka da kididdigar yara miliyan 10 da ba sa zuwa makaranta a arewa, yana mai cewa, dole ne kowa ya tashi tsaye don magance wannan kalubalen.